Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) ta fara karɓar buƙatun neman aiki na shekarar 2026, inda ake ɗaukar ma’aikata a rukunonin Mataimakin Jami’in Kiyaye Haɗurra (RMA), Sufeton Kiyaye Haɗurra (MI), Jami’ai (Officer Cadre) da kuma Likitoci (Officer – MBBS).
A matsayin wani ɓangare na tsarin neman aikin, ana buƙatar masu neman aiki su fara ƙirƙirar asusu a shafin ɗaukar ma’aikatan FRSC kafin su cika fom ɗin neman aikin.
Sai dai, bayan kammala rajistar farko, mutane da dama sun koka cewa ba sa samun saƙon imel na tabbatar da rajista, wato Activation Email, duk da sun duba akwatin saƙonsu da kuma ɓangaren Spam a imel.
Dalilin da ya sa ba ka samun saƙon tabbatar da rajista ba:
Rahotanni daga masu neman aikin sun nuna cewa matsalar ba ta shafi mutum ɗaya ba, domin ta zama ruwan dare ga mutane da yawa. Hakan na nuna cewa matsalar na iya kasancewa daga tsarin aikin ɗaukar ma’aikatan FRSC, ba wai kuskuren masu neman aikin ba.
Kafin ka ɗauki wani mataki, ka tabbatar ka bincika:
Akwatin saƙonka (Inboɗ), Spam ko Junk, Promotions ko Social (ga masu amfani da Gmail).
Idan har yanzu ba ka ga saƙon ba, ana ba da shawarar ka bi waɗannan matakan.
Kada ka riaa dannawa sau da yawa don sake turo saƙon.
Masu neman aiki an shawarce su da kada su riƙa dannawa akai-akai kan zaɓin “Resend Activation Email”.
Yawan yin hakan ba ya hanzarta isowar saƙon, kuma yana iya kawo cikas ga tsarin aika saƙon.
Ka jira kafin ka sake neman a turo saƙon:
Idan ka taɓa amfani da zaɓin sake turo saƙon, yana da kyau ka jira tsakanin awa 5 zuwa awa 24 kafin ka sake gwadawa.
Wasu daga cikin masu neman aikin sun bayyana cewa sun samu saƙon ne bayan sun jira na wasu sa’o’i.
Guji yawan neman sake turo saƙon:
Rahotanni sun nuna cewa yawan neman a sake turo saƙon cikin ɗan lokaci kaɗan na iya hana tsarin karɓar sabon buƙata.
Ko da yake Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) ba ta tabbatar da hakan a hukumance ba, mutane da dama sun ce sun fuskanci irin wannan matsala.
Kada ka sake yin rajista da wani sabon adireshin imel:
Masana sun ce yin sabon rajista da wani adireshin imel ba zai magance matsalar ba.
Dalili kuwa shi ne, Lambar Shaidar ɗan ƙasa (NIN) ɗinka ta riga ta haɗu da rajistar farko.
Saboda haka, sake yin rajista na iya haifar da rajista sau biyu ko kuma ya hana ci gaba da neman aikin.
Yadda tsarin rajistar FRSC ke aiki:
Bayan kammala rajistar farko a shafin ɗaukar ma’aikatan FRSC, tsarin zai turo maka da saƙon imel mai ɗauke da:
Hanyar tabbatar da asusun (Activation Link),.Sunan mai amfani (Username), Kalmar sirri (Password).
Da zarar ka karɓi saƙon, sai ka kunna asusun, ka shiga shafin da bayanan da aka ba ka, sannan ka ci gaba da cike sauran bayanan da ake buƙata, ciki har da loda takardun da ake nema kafin ka mika buƙatarka.
Har yanzu ana ci gaba da ɗaukar ma’aikata:
Hukumar ta tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da karɓar buƙatun neman aikin na shekarar 2026.
Ana karɓar masu neman aiki a rukunonin:
Mataimakin Jami’in Kiyaye Haddura (RMA), Sufeton Kiyaye Haɗurra (MI), Jami’ai (Officer Cadre), Likitoci (Officer – MBBS).
An shawarci masu neman aiki da su kammala rajistarsu kafin wa’adin rufe karɓar buƙatu, tare da bin bayanan da Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) ke fitarwa a hukumance kawai.
Shawara ga masu neman aiki:
Idan har yanzu ba ka samu saƙon kunna asusunka ba, ka yi haƙuri, ka guji yawan neman a sake turo saƙon ko kuma ƙirƙirar sabon asusu da wani adireshin imel.
Tun da matsalar ta shafi mutane da dama, akwai yiwuwar tsarin ne ke fuskantar jinkiri.
Haka kuma, ka ci gaba da duba akwatin saƙonka, ciki har da Spam da Junk, domin saƙon daga Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) na iya shigowa a kowane lokaci.
