
Daga BELLO A. BABAJI
Wasu fusatattun matasa da suka shirya zanga-zanga, sun cinna wa babban ofishin ƴan sanda wuta, wanda ke yankin Ifon a ƙaramar hukumar Ose ta Jihar Ondo.
Lamarin ya biyo bayan mutuwar wani yaro ne a ofishin bisa zargin lakaɗa masa duka da aka yi har ya sheƙa lahira.
Masu zanga-zangar sun samu labarin mutuwar yaron ne, wanda aka garzaya da abokinsa zuwa asibiti tare da kwantar da shi a ɗaki na musamman, lamarin da ya haifar da fushin nasu da ɗaukar doka a hannu.
Haka kuma an samu wani gida a yankin ofishin, wanda shima an cinna masa wuta a yayin hayaniyar.
A game da al’amarin ne Kwamishinan ƴan sandan jihar, Wilfred Afolabi ya garzaya garin da abin ya faru domin tabbatar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
