
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i murnar cika shekaru 65 a duniya tare da yaba wa hazaƙarsa wajen ciyar da ƙasa gaba.
A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Kakakinsa, Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu ya bayyana El-Rufa’i a matsayin magabaci na gari kuma gogaggen ɗan siyasa.
Ya yaba wa gudunmawarsa ga harkar demokraɗiyya, hidima wa ƙasa da kuma ƙoƙarin gina matasa.
Ya kuma yabi ƙoƙarinsa yayin tattauna batun samar da jami’iyyar APC da gudunmawar da ya bayar a nasarorin da ta samu a zaɓukan 2015, 2019 da 2023.
Shugaba Tinubu ya yi masa fatan samun lafiya mai ɗorewa da ƙarfin cigaba da yi wa ƙasa hidima.
El-Rufa’i ya taɓa riƙe muƙamin ministan Abuja da kuma Darakta-Janar na Hukumar Kula da Masana’antu daga shekarar 2003 zuwa 2007.
