Shugaban NULGE a Katsina ya taya zaɓaɓɓun ciyamomi murnar lashe zaɓe

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa reshen Jihar Katsina, Nasiru Wada Mai’Adua ya taya zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi 34 na jihar murnar lashe zaɓe.

A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa, ya ce sabbin ciyamomin suna da rawa da za su taka wajan kyautata aikin ma’aikatan ƙananan hukumomi a jihar.

Nasiru Mai’adua ya kuma yi kira a gare su da su duba yadda ayyukan yau da kullum ke gudana a ƙananan hukumominsu tare da fito da tsare-tsare da za su ɗaukaka darajar aikin a ƙananan hukumominsu.

“Ya kamata su fito da tsare-tsare ta yadda ƙananan hukumomin za su rinƙa gina wa ma’aikatansu gidaje kamar yadda takwarorinsu a matakin jiha da ƙasa ke ginawa a kowacce jiha.”

Ya kuma yaba wa gwamntin Dikko Raɗɗa kan yadda ta ke biyan ma’aikatan ƙananan hukumomin bai ɗaya da takwarorinsu na jiha kuma akan lokaci.

Shugaban NULGE’n ya ce ƙungiyarsa a shirye take ta haɗa gwiwa da shugabannin ƙananan hukumomin domin kyautata rayukan ma’aikata da al’umma baki ɗaya.

Ya yi kira ga ƴaƴan ƙungiyar da su cigaba da bai wa ciyamomi haɗin kai domin samar da ci-gaba a jihar.

By Babaji