Galihu: Yara 26,000 ake tsarewa a gidajen yari duk shekara a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Masu ruwa da tsaki da suka haɗa da Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta ƙasa (NJC), Hukumar Kula da Yara ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNICEF) da kuma Hukumar Bayar da Agaji ta Nijeriya (NEMA) sun yi kira da a mayar da matasan da suka aikata laifi zuwa wuraren gyaran hali, maimakon a yanke musu hukunci zama a gidan yari.

A zaman taron jama’a karo na biyu na kwamitin bincike mai zaman kansa kan zargin cin hanci da rashawa, azabtarwa, zalunci, wulaƙanci da cin mutuncin da Hukumar Gidajen Yari ta Nijeriya (NCoS) ke yi, wanda aka gudanar a ƙarshen mako a Abuja, masu ruwa da tsakin sun yi kira da a gaggauta aiwatar da dabarun da suka wajaba wajen gyaran hali ga matasa.

Wakiliyar UNICEF, Nkiru Maduechesi, wanda fa yi magana, ta bayyana cewa, binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa adadin yara ƙanana a gidajen yarin Nijeriya na da matuƙar tayar da hankali.

Ta ce, a kowace shekara, yara da matasa 26,000 (wato ‘yan ƙasa da shekaru 21) ne ake ajiye su a gidajen yari, kuma kashi 74 cikin 100 na su suna jiran shari’a.

“Dukkanmu mun san cewa abu na musamman game da yara shi ne cewa rayuwarsu tana da faɗi, kuma yayin da aka hana su ilimi da lafiya a tsare, rayukan yaran za su gurɓata, za su rasa dama ɗaya tilomda su ke da ita.

Don haka, ta ba da shawarar haɗa gwiwa da duk masu ruwa da tsaki don ɗaukar hanyoyin gyaran hali cikin gaggawa don ɗaukaka waɗannan yara da kuma sanya su zama nagartattun mutane.

Maduechesi ta yi nuni da cewa, “wannan matsalar ta wuce ma’aikata ɗaya ko kuma hukuma ɗaya;

“Game da ƙalubalen da ake fama da shi a fannin lafiya, wani lokaci mai martaba a wannan bangaren (jami’an gyaran hali) ba ya da wani taimako saboda takardar da ‘yan sanda suka gabatar za su ce yaron yana da shekara 18, amma a gaskiya yaron bai cika shekara 18 ba.

“Batun dokar kafa cibiyoyin tallafi a Nijeriya na buƙatar a sake duba wannan doka domin wannan dokar ta kai shekara ta 1962. A lokacin ne aka kafa ta, kuma ba a sake yin nazari ba, don haka, ina ganin idan muna da doka mai kyau, za ta buƙaci a samar da kyakkyawar manufa da aiki.”

Shugabar kwamitin kuma babban sakatare na ma’aikatar harkokin cikin gida ta tarayya, Dakta Magdalene Ajani, ta bayyana muhimmancin ilimantar da fursunonin da ake tsare da su.

Ta ce, hukumar ta NCoS na samun ci gaba a wannan fanni sakamakon haɗin gwiwa mai ƙarfi da ta samu da masu ruwa da tsaki kamar su Jami’ar NOUN, Hukumar Jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC), da ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGO), waɗanda ke karɓar wasu kuɗaɗe na ilimi.

Ta kuma buƙaci mahukuntan hukumar ta NCoS da su nemi aikin ɗaukar malamai domin koyar da sana’o’i da sauran ayyukan hannu ga fursunonin.

“Muna da kyau a fannin ilimi ta yadda muna da haɗin gwiwa daga dukkan cibiyoyin ilimi, walau WAEC, NECO,  Jami’ar NOUN, a shirye suke su haza kai da mu, da gudanar da ayyuka, da karɓar kuɗaɗen fursunonin domin kada su kashe kuɗi.

Sakataren kwamitin kuma wanda ya kafa ƙungiyar farfaɗo da fursunoni da walwala (PRAWA), Dakta Uju Agomoh, ta bayyana cewa ɓangarori biyu na tattaunawa da kwamitin su ne batutuwan marasa galihu da ake samu a wuraren da ake tsare da su, musamman wuraren gyaran hali, da sauran batutuwan da suka shafi mata, masu taɓin hankali, da kuma nakasassu a gidajen yari.

Ta ce, akwai buƙatar a gaggauta aiwatar da sashe na 33 da na 34 na dokar hukumar gyaran hali ta Nijeriya da kuma tanade-tanaden da aka samu a ƙarƙashin sashe na 13 da sashe na 14 na dokar hukumar gyaran hali ta Nijeriya kamar yadda ya shafi batun.

By ukarofi