Gwamnoni sun nemi Tinubu ya jinkirta biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomin kai tsaye

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnonin Jihohi sun ƙaddamar da wani sabon yunƙuri na ƙalubalantar shirin rabon kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya ga ƙananan hukumomi kai tsaye a wani sabon yunƙuri na jinkirta aiwatar da hukuncin da Kotun ƙoli ta yanke kan cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Wasu daga cikin gwamnonin, a wata ganawa da suka yi da shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja, ranar Talatar da ta gabata, sun nuna rashin amincewarsu da biyan kuɗazen kason ƙananan hukumomi da babban bankin Nijeriya ke yi, saboda buƙatar magance basussukan biliyoyin daloli da ake zargin su da almubazarancin sa.

Jami’an fadar shugaban ƙasar sun ce gwamnonin sun yi amfani da damar liyafar buɗa baki wajen tunkarar shugaban ƙasar tare da sabunta tattaunawa kan rabon kuɗaɗen kai tsaye ga ƙananan hukumomin, wanda aka samu tsaiko.

“Lokacin da gwamnonin suka zo ranar Litinin don yin buɗe-baki, sun nemi ganawa da shugaban ƙasar, wanda suka yi a ranar Talata da yamma.”

Da yake magana bisa sharaɗin sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana a kan lamarin, wani jami’in da ya ke ba da cikakken bayani ya ci gaba da cewa, “A ƙarshe sun gana da shugaban ƙasar a ranar Talata domin neman mafita.

“Abubuwa biyu ne ke faruwa Gwamnatin Tarayya tana son CBN ya biya kason, kuma duk ƙananan hukumomi su buɗe asusun ajiya da CBN.

“Amma gwamnonin sun ce a’a ba sa so haka, sun ce idan kuɗin ya tafi CBN, kamar yanzu Gwamnatin Tarayya ke sarrafa komai.”

Wata majiya mai tushe ga tattaunawar da Tinubu ya yi da gwamnonin ta nuna cewa gwamnonin jihohin sun buƙaci a aika kuɗaɗen ne a asusun banki na kasuwanci.

“ɗaya daga cikin gwamnonin ya ce da CBN ke tafiyar da asusun, za su buƙaci amincewa daga Babban Akanta, kuma ba sa son hakan a bankunan kasuwanci,” inji majiyar.

Dangane da sakamakon taron, jami’in ya bayyana cewa, “sun ce taron ya yi kyau amma ba a san abin da suka amince da shi ba.

A tarihance dai an daɗe ana cece-kuce kan batun samar da kuɗaɗe na ƙananan hukumomi, musamman saboda yadda ake samun saɓani a tsakanin gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi.

A ranar 11 ga Yuli, 2024, Kotun Koli ta yanke hukuncin da ya tabbatar da cin gashin kan kasafin kuɗi na ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar.

By ukarofi