Gwamnatin Sakkwato ta rage farashin buhun shinkafa 50kg zuwa N48,000

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bullo da shirin sayar da shinkafan tallafi a kan Naira 48,000 kan kowacce buhu mai nauyin 50kg ga mazauna yankin, da nufin samar da abinci.

Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata a cikin wata sanarwa, inda ya jaddada cewa shirin wani ɓangare ne na hadin gwiwar gwamnati da masu hannu da shuni da masu ruwa da tsaki.

An sanar da wannan ci gaban ne biyo bayan ƙaddamar da rabon kayan tallafi da gwamnatin jihar ta yi a hukumance ga mabukata da marasa galihu a faɗin jihar Sakkwato.

Gwamnan ya yi wannan aikin ne don aarfafa himmarsa ga jin daɗin jama’a da gudanar da mulki cikin tsari.

Gwamnan ya bayyana cewa samar da kayan abinci, tallafin kuɗi, da babura ga mabukata ya samo asali ne sakamakon karamcin masu hannu da shuni.

“Bugu da ƙari, mun gabatar da sayar da tallafin shinkafa kan Naira 48,000 kan kowacce buhu 50kg domin samun sauƙin abinci ga mutanenmu.

“Wannan shiri da aka yi a cikin watan Ramadan mai alfarma, ya nuna irin sadaukarwar da muka yi na rage wahalhalu da kuma samar da al’umma mai tausayi da juriya.

“Ina miƙa godiya ta ga dukkan masu hannu da shuni da suka haza kai da mu a wannan kyakkyawar manufa,” inji shi.

Gwamnan ya kuma tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa, tare, jihar za ta ci gaba da ɗaukaka waɗanda suka fi fama da talauci.

Wannan ci gaban ya zo ne kwanaki bayan da gwamnatin jihar Sakkwato a watan Fabrairun 2025, ta fitar da wani shiri na tallafin kayan abinci na Naira biliyan daya domin samar da kayayyaki masu sauƙi ga ma’aikatan gwamnati da masu ƙaramin ƙarfi a faɗin ƙananan hukumomi shida.

Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu Alhaji Ibrahim Dadi-Adare ne ya bayyana hakan yayin wani taron horas da masu shaguna a ranar Litinin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ta ruwaito.

Ya bayyana cewa shirin yana da nufin sauƙaƙe nauyin kuɗi na siyan kayan abinci masu muhimmanci da inganta jin daɗin ma’aikata.

“Gwamnatin jihar Sokoto ta ƙaddamar da shirin tallafin kayan abinci na Naira biliyan ɗaya da nufin samar da kayayyaki masu sauƙi ga ma’aikatan gwamnati da masu ƙaramin ƙarfi a ƙananan hukumomi shida da ke faɗin jihar.

“Da yake magana a wani taron horar da masu gudanar da shaguna a ranar Litinin, kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, Alhaji Ibrahim Dadi-Adare, ya jaddada cewa an tsara shirin ne domin inganta jin daɗin ma’aikata,” inji rahoton NAN.

By ukarofi