Matsin rayuwa: ’Yar NYSC za ta fuskanci tsawaita hidimar kwanaki 30 kan sukar Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata ‘yar Legas mai yi wa ƙasa hidima (NYSC), Ushie Uguamaye, za ta iya fuskantar tsawaitar wa’adin hidima na tsawon kwanaki 30 tare da rabin albashi sakamakon sukar da ta yi wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Za a aiwatar da hakan ne bisa dokar NYSC na Bye Laws ‘Reɓised 2011’.

A kwanakin baya, Uguamaye, wacce aka fi sani da ‘talktoraye’ a Tiktok, a wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na tiktok ranar Asabar, ta bayyana damuwa kan taɓarɓarewar tattalin arziki a Nijeriya inda ta nuna takaicinta kan yadda jajircewa ke neman zama aikin banza.

Ta kuma fito fili ta soki gwamnatin Bola Tinubu inda ta bayyana shi da “mugun shugaba,” sannan ta kuma ta dasa ayar tambaya kan shirin gwamnatin na yayewa ’yan ƙasar talaucin da ke damun su.

Har wa yau, ’yar bautar ƙasar da ke zaune a birnin Legas, ta bayyana birnin da “jiha mai wari” tana mai ƙorafi da gurɓacewar iska da cunkoson da jihar ke fuskanta.

To sai dai kuma jim kaɗan bayan bidiyon nata, sai ta sake fitar da wani inda take bayyana cewa tana fuskantar barazana daga hukumar yi wa ƙasa hidima bisa kalaman nata.

“Ya ku ‘yan uwana ’yan Nijeriya, sun saurari bayanina. Idan ba ku ƙara jin ɗuriyata ba a intanet , kun san wa za ku kama da laifi. Ban yi wani abun da ba daidai ba kawai dai na nemi da su yi wani abu kan hauhawar farashi.”

Me zai hana ni yin magana? Kasancewar mutum mai yi wa ƙasa hidima bai ba ya nufin na sarayar da ’yancina na yin ƙorafi,” inji Ushie Rita Uguamaye.

Ta kuma nuna hoton saƙon da aka ce ta samu daga jami’an NYSC na gayyatar ta zuwa ofishin ƙaramar hukumar Eti-Osa a ranar Litinin.

A cewar Uguamaye, tana tsoron ranta saboda itama tana samun barazana daga wasu da ba a san ko su waye ba bayan bidiyon nata ya yaɗu.

Bidiyon farko da Uguamaye ya yaɗa na iya saba wa dokar NYSC na Bye-Laws (Reɓised 2011), sashin da ya ce mambobin NYSC ba za su iya sukar masu riƙe da madafun iko ba.

An ce: “Duk wani memba da ya yi rashin kunya ga hukumar da aka kafa, kwamitin ladabtarwa na NYSC zai gurfanar da shi, kuma, idan aka same shi da laifi, za a iya tsawaita wa’adin aikin sa na tsawon kwanaki talatin (30) tare da rabin albashi.”

By ukarofi