Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Ogun

Spread the love

Rundunar ’yan sanda a jihar Ogun ta tabbatar da mutuwarta ɗaya daga cikin jami’anta a lokacin da yake bakin aiki a ƙaramar hukumar Ota na jihar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ’yan sandan jihar Omolola Odutola ta fitar, ta ce tuni aka fara bincike domin gano yadda lamarin ya auku.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne ranar Juma’a 14 ga watan Maris.

“Jim kaɗan bayan mun gaisa da shi, sai ya shiga ban-ɗaki amma bayan wasu lokuta – kawai sai na ji ƙara harbin bindiga, inda na ruga na je na kuma tarar da Oloyede cikin jini,” a cewar wani jami’in ɗan sandan da lamarin ya faru a idonsa.

Ya ce daga nan suka garzaya da shi asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

“An gano bindigar da ya yi amfani da ita wajen harbe kansa, gawarsa kuma na ajiye a asibiti don ci gaba da bincike,” inji sanarwar ’yan sandan.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Lanre Ogunlowo ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin don gano cewa ko marigayin yana da wata matsala ta lafiyar ƙwaƙwalwa.

By ukarofi