Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta tabbatar da cewa wata yarinya ‘yar shekara 16 mai suna Maryam Samuel ta kashe kanta a unguwar Kaltungo da ke ƙaramar Hukumar Kaltungo a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Buhari Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar a Gombe, ya ce yarinyar ta kashe kanta ne ta hanyar rataye a kan bishiya.
Ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 14 ga watan Maris, bayan sa’o’i 24 da marigayiyar ta bar gida zuwa ɗebo itace.
“A ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9:00 na safe ne hakimin ƙauyen Kalarin ya kai rahoton lamarin a hedikwatar shiyya ta Kaltungo.
“Marigayiyar daga baya aka bayyana sunansa da Maryam Samuel, ‘yar shekara 16 daga unguwar Kalarin, ta rataye kanta da igiya a kan bishiya a tsaunin Kalarin,” inji shi.
Abdullahi ya ce an ajiye gawar a babban asibitin Kaltungo.
Ya ce, binciken farko da aka yi ya nuna cewa marigayiyar ta bar gida ne a ranar Alhamis don dibar itace daga daji da ke kusa da wurin, inda ya ƙara da cewa bincike zai gano musabbabin faruwar lamarin.
Sai dai wata majiya daga dangin marigayiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa manema labarai cewa yarinyar tana ɗauke da juna biyu da saurayinta ya ɗirka mata, lamarin da ya harzuƙa iyayenta.
Majiyar ta ce, an gano yarinyar tana ziyartar masoyinta ne, kuma tana ɗauke da juna biyu a yayin wata mu’amala tsakaninta da saurayin.
