Wani abu da ya kamata a sani game da cutar hawan jini

Tare da CHIROMA AMINU ASID

Bayani kan cutar hawan Jini:

Mene ne hawan jini?

Cutar hawan jini ita ce buguwar zuciya ya wuce adadin da ake buƙata.

Ciwon hawan jini yana ɗaya daga cikin cutuka masu haifar da illoli a jiki daga ciki har da rasa rai, domin ya na kashewa nan take.

A ƙa’ida fa, hawan jini kashi 85 ba asan abunda ke haddasa shi ba.

Alamomin da za a fahimci akwai alamun hawan jini sun sha bamban da illolin da yake haifarwa.

Hawan jini yana zubar da ciki, ya tsotse jini, ya haddasa tsinkau tsinkau, ya sa ciwon sashe dama rasa rai.

Mai cutar hawan jini zai iya zama da illolin da hawan jininsa ya haddasa masa ko da kuwa an warke daga hawan jinin.

Rashin ji, rashin gani da karkacewar baki ko karyewar harshe na daga cikin sauran illolin hawan jini.

A ƙa’ida ta hawan jini, ba a tabbatar da shi ga wani sai da abun awonsa, alamomin sa kaɗai ba sa tabbatar da shi.

Faɗuwar gaba, zafin ƙirji, rashin bacci, kumburin ƙafafu ko jiki, ciwon kai da hauhawan bugun zuciya na daga cikin alamominsa.

Matakai biyu waɗanda ke saurin saukar da hawan jini shine ai ta fitsari nan take sannan a bar gishiri.

Rashin yin fitsari na daga cikin ababen da ke ta’azzara matsalar hawan jini.

Cutar hawan jini tana daga cikin cutukan da ake gado daga uwaye da kakanni, amma ba lallai kuma kowa ya samu matsalar ba.

A sha ruwa lafiya.