Ingancin hadisai: Ahad da Mutawattir

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ 

A ilmul Hadith, malamai sun kasa hadisai zuwa azuzuwa guda biyu, wato Ahad da Mutawwatir. Ahad Hadith shine wanda marubuta hadisi suka saka a littafansu Mai jerin carbi guda daya na maruwaita, wato wane ya ji daga wane har zuwa ga manzo. Maruwaitan kuma sun ruwaito daga sahabi guda. Shi kansa irin wannan hadisi na Ahad ya kasu kashi uku: Akwai Mashhur, Aziz da Gharib. Amma duk ba su kai Mutawwatir ba wajen inganci.

Shi kuma mutawattir, hadisi ne da ya zo ta jerin carbi fiye da daya, wato akan sami jerin carbin maruwaita daban daban daga biyar zuwa shida. An fi gansuwa da irin wannan hadisi saboda ganin cewa da wahala a ce maruwaita daban daban a jerin carbi masu yawa su tattaru wajen ruwaito abin da ba haka bane, ko hadisin karya.

Abin tambaya shine menene dalilin da malamai suka saka wasu tsauraran matakai kafin a yarda da sahihancin hadisi? Magana ta gaskiya ita ce saboda a lokacin da su Bukhari da Muslim ke wannan aiki, hadisai na karya da bara-gurbi su ne mafi yawan hadisai da su ke yawo a tsakanin musulmi. Abinda zai tabbatar maka da haka shine, lokacin da su Bukhari su ka yi aikin tattara hadisi, ya tattaro hadisai 600,000 daga malamai daban daban, sannan ya ginawa kansa tsarin tantance su. Akwai malamin da ya je karbar hadisi wajensa aka ce ya na garken tumaki, da ya zaga sai ya ga ya na cunawa akuya zangarniya, ta na zuwa ya cafke ta. Wannan hali na yaudarar dabba ya sa Bukhari ya fasa karbar hadisi wurinsa. Wannan ne irin tsantseni da su ka nuna wajen tantance hadisi. To a cikin 600,000 da ya ruwaito, bayan tankade da rairaya, kasa da kashi 1% kacal ya iya amincewa ya saka a Sahihinsa ya yi watsi da kashi 99%. Kuma a cikin wadanda ya aminta ya saka akwai wadanda abokin aikinsa Muslim, ya ki amincewa da su a cikin nasa sahihin.

Misali Muslim ya ruwaito hadisin Rajamu amma Bukhari bai karbe shi ba; Muslim ya ruwaito hadisin wasiyyar Annabi ta Qurani da Ahlul bayt amma Bukhari bai yi ba; Muslim ya ruwaito hadisin Mutum bakwai karkashin al’arshi ranar kiyama, Bukhari bai yi ba. A nasa bangaren Bukhari ya aminta da ruwaito hadisin tafiyar Isra’i da Mi’iraj amma Muslim bai ruwaito ba; Ya ruwaito halittar Adam daga zati amma Muslim Bai ruwaito ba; Sannan Bukhari ya ruwaito hadisin da ke nuna fifikon zamani daga kan sahabbai sai tabi’ai haka-haka, amma Muslim bai ruwaito ba. Dalilin wannan sabanin shine kowannensu akwai irin matakai na aminci da ya dogara da su, duk da cewa sun rayu zamani guda, har ma suna da malamai iri daya domin Imam Ahmad Bn Hanbal, Yahya Bn Ma’in da Ali Ibn Al Madini sun koyar da Bukhari da Muslim. Kuma a cikin littafinsa “Kitab Al Tamyiz” Imam Muslim ya ambaci Imam Bukhari a ciki. 

To idan muka koma kan hadisai mutawattir, wadanda maruwaita su ka kawo masu jerin carbi da yawa, a tarihin hadisai kaf, ba na jin akwai wani hadisi mutawattiri da ya kai na hajin ban kwana. Domin ba’a taba samun hadisin da aka fada a bainar jama’a masu yawa kamarsa ba. Wata kididdigar na cewa sahabbai 100,000 su ka halarci wannan haji su ka saurari hudubar Manzo ta karshe. To shi kansa wannan mashahurin hadisi, ku biyo ni kuga yadda yazo da ruwaya mabanbanta.

Cikin littafin Mishkah Al Masabih (Littafin Hadisai wanda Mohammad Ibn Abdullah Al Tabrizi ya hada) littafi na 10 hadisi na 49 wanda Jabir Bn Abdullahi ya ruwaito na hajin ban kwana, dogon hadisi ne amma a wajen karshe sai ya ke cewa “…Na bar muku littafin Allah (Qurani) Wanda idan ku ka yi riko da shi ba zaku taba bata ba.  Idan an tambaye ku game da ni, me za ku ce? Sai su ka amsa “Mun shaida ka isar da sakon da aka baka” Sai Annabi ya daga Dan yatsansa ya nuna sama sannan ya nuna mutane ya ce “Ya Allah ka shaida; Ya Allah ka shaida” ya fada har sau uku.

Can kuma a cikin Muwatta littafi na 46 hadisi na 6 an ruwaito cewa ga abinda Annabi ya ce a wajen hudubarsa ta ban kwana “Na bar muku abubuwa guda biyu. Matukar kun yi riko da su, ba za ku karkace daga hanya ba. Su ne littafin Allah da sunnar manzonsa”

To ba a Muwatta kadai aka ruwaito wannan hadisi ba, Abu Dawud a hadisi na 1905 shi ma haka ya ruwaito exactly, wato Annabi ya bar Qurani da Sunnah.

To ba fa a nan lamarin ya tsaya ba domin sai kuma ga shi a cikin Sunan Al Tirmidhi shi kuma ga abinda ya ruwaito a hadisi na 3788 “Na bar muku abubuwa guda biyu. Matukar Kun yi riko da su, ba za ku karkace daga hanya ba. Su ne littafin Allah da Ahlul bayt”. Shi wannan ɓersion din, ba Tirmidhi kadai ya ruwaito shi ba, domin a cikin Musnad Ahmad hadisi na 18407 shi ma ya ruwaito wannan thaqalain din na “Qurani da Ahlul bayt.

Kun ga cewa ruwaya iri uku ta fito a hadisi guda daya da Annabi ya fada a gaban dubban daruruwan mutane. Wato cewa ya bar mana:

1. Qurani

2. Qurani da Sunnah

3. Qur’ani da Ahlul baiti 

Ya ilahi, idan mutawattirin hadisi mafi shahara cikin hadisai zai shiga wannan rudani, ina kuma ga wadanda ba su kai shi ba, ballantana Ahad Hadith?

Sannan masu tada jijiyar wuya akan maganar hadisi da su ke kokarin daidaita ingancinsa da Qurani, duk manyan Malaman Salaf tun daga Shafi’i har zuwa kan Malam Abubakar Gumi (wanda ya kawo mana izala Nigeria) ba wanda bai nuna cewa Qurani ne kadai babu kuskure cikinsa ba. Sannan don Allah akwai basalafen da a cikin wadancan hadisai na ban kwana wanda zai iya amincewa har zuci da a aikace da hadisin Jabir wanda Muslim ne ya ruwaito cewa Annabi Qurani kawai ya yi wasiyyar bar mana? Ko kuma hadisin Tirmidhi da Ahmad da su ka ce ya mana wasiccin riko da “Qurani da Ahlul bayt”? 

Wannan mashahurin hadisi da babu kamarsa shi ya raba mu gida uku, wato mabiya Qurani zalla, Sunna da Shi’a. Shin idan mutawattirin hadisi zai sami wannan Shubha, ya ilahi ina ga hadisi Ahad? Zai yiwu Annabi a waje guda a gaban dubban daruruwan mutane ya fadi hadisi wanda a karshensa zai fadi mabanbantan abubuwa guda uku?

Mu fa ba yaki da hadisi mu ke yi ba,  domin ba Manzon Allah ba ma, ko malamin zamanin mu ya zo da magana sai mu karba da gudu, matukar bata yi karo da Qurani ko Ilimi ko hankali ba. Abinda ake kira shine, mu rungumi umarnin Allah na gane ni’imar da yayi mana ta kwakwalwa tare da bin umarnin tafakkuri da tadabburi da Allah ya yi ta mana a Qurani, umarnin da ya zarce kowane irin umarni. Duk hadisin da ya ci karo da Qurani, mu sani cewa lallai babu yadda za a yi Annabi ya karyata sakon da ya kawo. Sannan idan hadisi ya ci karo da ilimi ko kimiyya ta zahiri shi ma mu ajiye shi. Domin hadisin kilili ya nuna mana cewa Annabi da kansa ya nuna a sha’anin ilimin zahiri na rayuwa ana iya yin sabanin abin da ya fada.

Kuma babban ƙalubaken Musulmi a yau shi ne rashin dabbaka abubuwan alherin da hadisan su ka assasa. Mu yi ta kwarmato a kan aƙida amma idan anzo maganar aikata kyawawan dabi’un Manzon Allah, kalilan cikinmu ke iyawa. Gaskiya, hakuri da mutane, amana, hadin kai, son juna, adalci, taimako ba riya da duk kyawawan dabi’u sun ƙaurace a cikin al’ummar mu. Kowa ya san cewa Imani sai da aiki, haka Allah ya fada mana cikin Qurani. Duk inda kaga amanu zaka ga amala, amma mu mun raba auren mun rungumi daya mun yi watsi da dayan, shi ya sa addinin ya kasa kai mu matsayin da ya dace a ce mun je, sai mu ke ta shiririta.

Allah ya ganar da mu. Jummu’a Mubarak!

Malam Ali manazarci ne a Kano

By ukarofi