Gidan Rediyo Kano ta cika shekara 80 da kafuwa

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gidan rediyo Kano, da ke Gidan Bello Ɗandago, na daga cikin gidajen rediyo na farko kuma mafi daɗewa a jihar Kano.

An kafa gidan rediyon ne a shekarar 1946, a matsayin reshen Radio Distribution Services (RDS) da Turawan Birtaniya suka assasa. Marigayi Alhaji Bello Ɗandago ne ya kasance jami’in farko na gidan rediyon.

A farkon kafuwarta, Radiyo Kano na isar da shirye-shirye ne ta hanyar lasifika a wuraren taruwar jama’a. Daga bisani, a shekarar 1958, aka girka na’urar watsa shirye-shirye mai karfin 1 kilowatt, wadda ta ba da damar isar da sauti a faɗin birnin Kano.

Cikar Rediyo Kano shekaru 80 na aiki wata muhimmiyar nasara ce a tarihin yaɗa labarai a Kano da ma Najeriya. Tsawon shekaru, gidan rediyon ya taka rawa wajen wayar da kan al’umma, musamman a lokacin gwagwarmayar neman ’yancin kai, tare da yaɗa ilimi da bayanai masu amfani.

Kazalika Rediyo Kano ya kasance wata makaranta ga al’umma, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen ilimi, faɗakarwa, wayar da kai da nishadantarwa, tare da zama wani ɓangare na rayuwar al’ummar Kano tsawon shekaru da dama.

A zantawarsa da manema labarai shugaban gidan Abubakar Adamu Rano ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen mayar da gidan cibiyar koyar da aiki jarida a Kano.

An dai gudanar dai gudanar da gagarumin taron cika gidan Radiyo shekaru 80 a jiya Asabar inda Sakataren Gwamnatin Kano Alhaji Umar Farouk ya wakilci Gwamna.

Haka kuma ya samu halartar tsofaffin shugabannin gidan Rediyon da suka haɗa da ƙwararren ɗan Jarida Alhaji Halilu Ahmad Getso da sauran manyan ƴan jarida da suka yi aiki a gidan.

By ukarofi

Leave a Reply