Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
ƙungiyar jin ƙai ta Gidan Alheri/Dangin Juna Afirka ta taimaka wajen fitar da mutum huɗu daga Gidan Gyaran Hali na Jihar Gombe bayan ta biya musu tarar kuɗi da diyya da kotu ta ɗora a kansu.
Waɗanda aka taimaka wa sun haɗa da matasa uku da mace ɗaya, waɗanda suka ci gaba da zama a gidan gyaran hali duk da hukuncin da aka yanke musu, sakamakon rashin ikon biyan tarar da diyya.
An gudanar da wannan aiki ne yayin wata ziyara da tawagar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Hon. Sagir A.A. Haruna, ta kai Gidan Gyaran Hali na Gombe, tare da wasu mambobi da suka haɗa da Barista Abubakar Haruna Anature, wanda ke cikin kwamitin da aka dorawa alhakin gudanar da irin waɗannan ayyukan alheri.
Da yake karɓar baƙuncin tawagar, Mataimakin Kwamturolan Gidan Gyaran Hali, DCC Victor Odafen, ya yaba wa ƙungiyar bisa wannan gagarumin taimako, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage cunkoson da ake fama da shi a gidan.
Ya bayyana cewa, an gina cibiyar ne domin daukar mutum 399 kacal, amma a halin yanzu tana ɗauke da sama da mutum 1,000, lamarin da ya sanya irin wannan gudunmawa ke da matuƙar muhimmanci.
“ƙungiyar Gidan Alheri ta tabbatar da ma’anar sunanta ta hanyar gudanar da ayyukan alheri masu anfani ga al’umma. Idan sauran ƙungiyoyi da masu hannu da shuni suka yi koyi da irin wannan aiki, hakan zai taimaka matuƙa wajen rage cunkoson da ake fama da shi a gidajen gyaran hali,” inji shi.
A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar, Hon. Sagir A.A. Haruna, ya ce kungiyar ta dauki taimakon mabukata a matsayin wata hanya ta neman lada da kuma share hawayen marasa ƙarfi a cikin al’umma.
Ya ce, ƙungiyar na ci gaba da tallafa wa masu bukata a duk lokacin da ta gano halin da suke ciki, gwargwadon damar da Allah Ya hore mata.
Har ila yau, ya yabawa mambobin ƙungiyar bisa sadaukar da dukiyoyinsu domin gudanar da ayyukan jin kai da tallafa wa marasa galihu.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa waɗanda aka taimaka wajen sakinsu sun aikata ƙananan laifuffuka ne, amma suka ci gaba da zama a gidan gyaran hali saboda rashin ikon biyan tarar ko diyya da kotu ta ɗora musu.
Baya ga taimakon sakin su, daya daga cikin mambobin ƙungiyar, Hauwa’u Abdulmumini Hasken Matan Gona, ta bai wa matar da aka saki tallafin jari tare da kayan sawa domin ta samu damar fara sana’a da kuma dogaro da kanta.
Mutanen da aka taimaka wajen sakinsu, waɗanda aka boye sunayensu, sun nuna matuƙar farin ciki tare da yabawa ƙungiyar Gidan Alheri/Dangin Juna Afirka, inda suka yi addu’ar Allah Ya saka musu da mafificin alheri.
