Gidauniyar ‘Giving Back Initiative’ ta raba wa mabuƙata kayan abinci a Sakkwato 

Spread the love

Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato

Kwamitin rabon tallafin da Gidauniyar tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Dr Attahiru Bafarawa, wacce a turance ake kira da Giɓing Back Initiatiɓe, ta kafa domin raba wa ‘yan gudun Hijira da mabuƙata kayan abinci da kuɗaɗe ya soma aikinsa da rabawa ‘yan gudun hijirar ƙananan hukumomin Rabah, Isa da Sabon Birni. 

Tun da farko sai da Shugaban Babban Kwamitin Malam Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato ya bayyana cewa an soma aikin ne tare da ƙaddamar da rabon kayan abinci ga sansanin ‘yan gudun Hijira na Gandi da ke Ƙaramar Hukumar Rabah. 

Shugaban ya kuma ƙara da cewa, Gidauniyar tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Dr Attahiru Bafarawa ta kafa kwamitin ne domin zaƙulo bayin Allah mabuƙata da za a tallafawa a fannonin  tallafin kayan abinci, kiwon lafiya, da samar da ruwan sha, da kuma samar da tallafin ilimi, sana’a da sauran su. 

Shirin tallafin da aka yi wa laƙabi da “Mayar da alheri da aikin alheri,” an ƙaddamar da shi ne tun a ranar Jumma’a 04/10/2024, da nufin sauƙaƙawa halin rayuwar da jama’a suka samu kansu a ciki na ƙunci da tsadar rayuwa. 

Sadaukin Sakkwato ya yi godiya ga Gwamnatin Jihar Sokoto, fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ‘yan kwamiti, da duk mai hannu a cikin wannan aiki na jin ƙan al’umma ya roƙi jama’a da su yi masu addu’a don sauke wannan nauyi da aka ɗora musu, cikin gaskiya da adalci. 

Wakilin Yarin Gandi, Alhaji Yahaya Kabir, Shugaban Kula da Sansanin Malam Ibrahim Ahmad, wakilin ‘yan gudun Hijira kuma Hakimin Tabanni, Malam Muhammad Lawal sun yi godiya ga wannan Gidauniya tare da addu’ar Allah ya saka wa tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Dr Attahiru Bafarawa da mafificin alkhairi. 

Jadawalin rabon kayan ya nuna cewa, a ƙaramar Hukumar Rabah an raba buhunan kayan abinci 250, ga iyalai 1,763 a sansanin ‘yan gudun Hijira 20 da ke Gandi da Rabah, sannan an raba musu kudi Naira Miliyan biyu da rabi. 

Yayin da aka raba buhunan abinci 300 ga iyalai 1,500, sannan kuma an raba kuɗi Naira Miliyan uku a sansanonin ‘yan gudun Hijira guda biyar da ke Ƙaramar Hukumar Isa. 

A ƙaramar Hukumar Sabon Birni kuma an raba buhunan kayan abinci 350 ga iyalai 1,700 a sansanoni bakwai da ke Sabon Birni, an kuma raba kuɗi Naira Miliyan uku da rabi.

Shugaban babban kwamitin, Malam Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato, ya bayyana cewa a yanzu an fara ne da wadannan ’yan gudun hijirar duba da ganin suna cikin tsananin buƙata, yayin da nan gaba kaɗan za a yi rabon na sauran ƙananan hukumomin 20 da suka rage. Sannan za a cigaba da sauran ayyukan jinƙai da ake gudanarwa.

Shugaban ƙaramar Hukumar Sabon Birni, wakilan Rabah da Isa, uban ƙasar Isa, wakilan Gandi, da Sabon Birni da wakilan ‘yan gudun Hijira duk sun yi godiya da fatan alheri ga wannan tallafi da suka samu. 

Tawagar na tare ne da rakiyar mambobin Babban Kwamitin rabon tallafin Gidauniyar Attahiru Bafarawa da suka haɗa da Alhaji Nasiru Bafarawa, Alhaji Ahmad Gyarafshi, wakilan yankunan Isa, Alhaji Basharu Isa Guyawa (Shugaban ƙungiyar Rundumar Adalci), jami’an kula da Sabon Birni, Farfesa Shu’aibu Gobir, na Gandi Malam Ibrahim Ahmad, tare da Malam Nura Attajiri, Malam Kabiru Shehu Binji, Sidi Gandi da Mukhtar A. Halliru.

Daga cikin waɗanda aka zanta da su sun yi godiya da addu’a, tare da kira ga sauran masu hali da su yi koyi da Garkuwar Sakkwato da irin ayyukan alheri da yake gudanarwa a ciki da wajen Jihar Sakkwato.

By ukarofi