Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Dattawan Arewacin Nijeriya (ACF) ta ɗauki matakin tunkarar ƙalubalen rashin tsaro da rashin haɗin kan da ke addabar Arewacin Nijeriya ta hanyar kafa kwamitoci na musamman guda biyu.
An ƙaddamar da kwamitocin ne biyo bayan ƙudurin da aka cimma a taron kwamitin amintattu na ACF da aka gudanar a ranar 4 ga Satumba, 2024.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙungiyar ta ACF, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar, kwamitin haɗin kai, zaman lafiya da sulhu, ƙarƙashin jagorancin Alhaji (Dr.) Yayale Ahmed, an umurce shi da ya gabatar da dabaru na haƙiƙa don samar da jituwa da tattaunawa a tsakanin al’ummomin Arewa.
Muhammad-Baba ya ce: “Wannan shiri ya samo asali ne daga damuwa game da taɓarɓarewar dangantakar ƙungiyoyi a yankin, wanda ya kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaba.”
Ya ce kwamitin na biyu da ya mayar da hankali kan tsaro yana ƙarƙashin jagorancin tsohon babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau (rtd).
“Wannan ƙungiya tana da alhakin samar da hanyoyin da za su iya magance matsalar rashin tsaro a yankin, wanda ya ci gaba da lalata rayuwa da rayuwa. Alhaji Mohammed D. Abubakar, tsohon Sufeto Janar na ’yan sanda, shi ne mataimakin kwamatin,” ya ƙara da cewa.
Jami’in yaɗa labaran ACF ya kuma bayyana cewa an ƙaddamar da kwamitocin ne a Abuja a ranakun 30 ga watan Satumba da 1 ga watan Oktoba, wanda Alhaji Bashir Dalhatu, Wazirin Dutse ya jagoranta.
Ya ƙara da cewa, “ana sa ran za su miaa rahotonsu a tsakiyar watan Nuwamba domin su sake nazari daga ƙungiyar ACF, inda daga bisani za su haɗa kai da gwamnonin jihohin Arewa da hukumomin tarayya don ganin an aiwatar da shawarwarin.”
