WGA ta haramta wa marubuta rubutu a kamfanin fim ɗin ‘Expendables’

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

A yayin da marubuta finafinai a Nijeriya ke fama da matsaloli da dama ta ɓangaren rashin sanin darajarsu, tauye haƙƙi da kuma yi masu yadda aka ga dama a finafinan da suka rubutuwa, kuma ba su da dama a ƙungiyance da za ta iya ƙwato masu haƙƙinsu, ko samar masu da ƙima da daraja kasancewar su ƙashin bayan kowane fim da za a yi.

Wannan na daga cikin dalilan da suka hana finafinan cikin gida tasiri tare da amo irin wanda ake sa ran zuwa yanzu su yi. Wannan matsala da har yau ke ci wa marubutan fim tuwo a ƙwarya ta kasance shuɗaɗɗiyar matsala a ƙasashen da suka samu ci gaba.

Daya daga ciki kuwa akwai ƙasar Amurka, inda masu harkar fim suke samun kuɗaɗe masu tarin yawa, tare da morar duk wata nasara da fim ɗin ya samu, kamar yadda muka yi darasi na musamman a wannan shafi a kwanakin baya kan yadda harkar fim ke tafiya a wasu ƙasashe da kuma yadda ake gudanar da ita a nan.

Kasar Amurka ƙarƙashin ƙungiyar Guild ta Amurka ta samar da kariya mai girma da kuma zama kariya, kuma uwa mai share hawaye ga marubutan da suke ƙarkashin rijistar ta, domin a ranar Larabar da ta gabata ne ƙungiyar ta Writers Guild ta Amurka ta umarci mambobinta da su guje yin aiki ga finafinan kamfanin Millennium, wanda ya shirya finafinai da dama, kamar dai ‘The Hitman’s Bodyguard’, ‘Expendables’, da sauransu. 

Kungiyar ta shaida wa mambobin cewa, kamfanin na da tarihin rashin biyan diyya na daga abinda ya rage, da kuma rashin biyan haƙƙi kan lokaci.

Kamfani da kuma ƙungiyar sun yi takun-saƙa kan sharuɗɗan da ya wajaba ya cika domin ya zama mai rattaba hannu kan ƙungiyar. Ya zuwa yanzu, bai sanya hannu kan yarjejeniyar 2023 na marubuta ba, wanda shi ne abin da ake buƙata don ɗaukar marubutan guild.

“Guild ta yanke shawarar cewa, Millennium ba shi da alhakin kuɗi, kuma yana buƙatar aika da isasshiyar yarjejeniya kafin saka hannu,” inji ƙungiyar. 

Ta ƙara da cewa, “Ya zuwa yau, Millennium, ya ƙi yin hakan.”

Aɓi Lerner ne ya kafa Millennium Films a cikin shekarar 1996, kuma ya tattara tare da yin manya-manyan finafinai da suka samu karɓuwa a duniya, domin baya ga finafinan ‘Eɗpendables’, ya kuma fitar da ‘Olympus Has Fallen’, ‘Bricklayer’, da kuma ‘The Mechanic’.

A cewar sanarwar WGA, ƙungiyar ta gabatar da ƙararraki da yawa akan kamfanin tsawon shekaru. ƙungiyar ta kuma buƙaci duk wani memba da ya yi aiki da kamfanin tun ranar 1 ga Mayu, 2023, ko aka tuntuɓe shi don yin aiki da shi, da ya sanar da ƙungiyar.

Kungiyar ta ce “Yana da matuƙar muhimmanci a hana Millennium tauye ƙa’idoji da haƙoƙƙin marubuta.

Matuƙar ba a kai ga matsaya ba, ba za a iya barin Millennium ta amfana daga ayyukan rubuce-rubucen da membobin WGA ke bayarwa ba.”

Saidai har zuwa lokacin mai magana da yawun Millennium bai magantu kan wannan hukunci na ƙungiyar Guild ta Amurka ba.

Gerard Butler, tauraron ‘Olympus Has Fallen,’ ya kai ƙarar Millennium a 2021 yana neman biya na musamman. An dai sasanta lamarin ba tare da kotu ba.

Hakazalika wani tsohon jami’in gudanarwa ya shigar da ƙarar cin zarafi ta fuskar jima’i a cikin 2017, yana zargin cewa Lerner ya haɓaka ƙin jinin mata da al’adar “ƙauna ta jima’i.”

A cikin 2013, kamfanin ya kai ƙarar WGA da marubuci Daɓid Callham a cikin taƙaddamar bashi akan fim ɗin ‘Eɗpendables’ na farko. Wanda kuma aka sasanta ba tare da zuwa kotu ba.

By ukarofi