Gidauniyar Kannywood ta yi jimamin rasuwar Nura Shariff

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gidauniyar Kannywood ta bayyana matuƙar alhininta game da rasuwar tsohon jarumi kuma manajan shirye-shirye a Masana’antar finafinai ta Kannywood, wato Nura Shariff.

Marigayin ya shahara ne da aikinsa a fina-finan da Kamfanin Abdul Amart ke shiryawa, ABNUR.

A cewar wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran gidauniyar, Yakubu Liman ya fitar, “Shariff ƙwararren mai fasaha ne wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa a bayan fage, lamarin da ya taimaka wajen samar da fina-finai masu nasara a Kannywood.”

Ta ce, “a matsayinsa na jarumi a kamfanin Iyantama a shekarun ’90s’, ya nuna ƙwarewa da hazaƙa da sadaukarwa a duk rawar da ya taka, abin da ya sa ya samu ƙauna da girmamawa daga masu kallo da kuma abokan aiki. A matsayinsa na manajan shirye-shirye, kuma an san shi da jajircewa da shugabanci nagari da kulawa da kuma inganci, yana mai tabbatar da cewa kowane aiki da yake jagoranta ya gudana cikin tsari da ƙwarewa.”

Kazalika, a tsawon rayuwarsa na aiki, marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen ɗaga darajar shirya fina-finai a Kannywood ta haɗin-gwiwa da Abdul Amart da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar.

Haka kuma, za a riƙa tunawa da Nura Shariff a matsayin mai tawali’u da karamci da kuma kyakkyawar mu’amala da ya nuna ga kowa, lamarin da ya sa ya kasance abokin aiki na gari, jagora abin dogaro, kuma aboki ga mutane da dama a masana’antar.

A ƙarshe, gidauniyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalai da abokai da abokan aikinsa musamman a kamfanin ABNUR da kuma sauran masoyansa a wannan lokaci mai cike da jimami da fatan Allah ya jiƙan sa ya kuma bayar da haƙurin juriyan rashin sa.

By Babaji