Daga JOHN D WADA, Keffi
Shugaban jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) na ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa Hon. John T. Teghtegh yace sakamakon zaɓen gundumomin babban birnin tarayya Abuja da aka kammala a ƙarshen mako da ya gabata inda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta yi nasara a kusan dukkanin gundumomin yankin bai zo masa da mamaki ba.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu jim kaɗan bayan bayyana sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta yi.
A cewarsa, jam’iyyarsa ta ADC ta sha kaye a zaɓen ne domin ‘ya’yan jam’iyyar ba su haɗa kai da kuma yin aiki tuƙuru domin samun nasarar su kafin zaɓe da lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓen ba.
Yace maimakon haka ‘yan jam’iyyar sun shagaltu ne kawai musamman da fafutukar neman muƙaman jam’iyyar daban-daban da sauran muradun kashin kansu maimakon haɗa kai da juna domin cimma burinsu na cin zaɓen.
Shugaban ya kuma yi nuni da wasu daga cikin kura-kuran jam’iyyar nasu waɗanda yace sun taimaka matuƙa wajen faɗuwa zaɓen da suka yi da suka haɗa da fara yaƙin neman zaɓe a makare da kuma rashin halartar ɗimbin ‘ya’yan jam’iyyar nasu ƙwansu da kwarkwata a lokacin kaɗa ƙuri’un kamar yadda akayi tsammani da dai sauransu.
Daganan sai Hon. John T. Teghtegh ya kuma yi amfani da damar yayi kira na musamman ga ɗaukacin ‘ya’yan jam’iyyar ADC ɗin dake babban birnin tarayya Abuja dama ƙasa baki daya da su yi koyi da wannan sakamakon zaɓen babban birnin tarayya Abuja sannan su ƙara jajircewa ta yadda za a haɗa kai da juna inda ya ƙara jadadda cewa koda yake farkon na iya kasancewa haka amma nan gaba akwai tabbacin cewa jam’iyyar ADC za ta taso kuma ta haskaka a manyan zaɓukan 2027.
