“Nasarorin da na samu na da nasaba da jajircewar da mahaifinmu ya yi kan ilimi”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Jajirtattun mata masu ƙwazo da himma kan duk abin da suka sa a gaba, su ne ake kira da Kallabi Tsakanin Rawwuna. Ba domin komai ba kuwa, sai don ƙoƙarin su da rawar ganin da suke takawa, wanda ko a cikin maza ma sai an tona kafin a dace da mai jarumtarsu. Hajiya Jamila Mu’azu Abubakar ɗaya ce daga cikin irin waɗannan matan da ake yi wa laƙabi da Giwar Mata. ƙwararriya ce kuma jajirtacciya kan fagen da aka fi saninta akai, wato fagen ilimi, inda take da gogewa akan ilimantar da ƙananan yara, da waɗanda suke samun rauni wajen fahimtar karatu. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya samu ganawa da ita a ofishin ta dake Jos, inda suka tattauna kan rayuwarta da gudunmawarta a ɓangaren inganta dabarun koyarwa, da ma ƙalubalen da harkar koyarwa ke fuskanta a Nijeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance.
MANHAJA: Za ki gabatar mana da kanki?
HAJIYA JAMILA: As salamu alaikum wa rhamatullah. Sunana Jamila Mu’azu Abubakar. Ni malamar makaranta ce, kuma uwa mai ba da tarbiyya. Ni ce shugabar makarantar Read World Class Academy da ke ƙarƙashin Gidauniyar Tallafawa Ilimi ta Farfesa Balarabe Yusha’u dake cikin garin Jos. Ni ce mai kula da ɗakin karatu na tunawa da marigayi Haruna ɗanbale, wanda yake ba da damar karatu da nazari ga mutane masu sha’awar neman ilimi, har ma da ɓangaren ƙananan yara. Harwayau kuma, ni ce jagoran ƙungiyar Arewa Early Readers dake samar da littattafan karatu na yara cikin harshen Hausa da Turanci, domin koyar da su Ilimi daga matakin farko. Ina da aure da yara uku, namiji ɗaya da mata biyu.
Ko za ki gaya mana wani abu daga tarihin rayuwarki?
Ni haifaffiyar garin Jos ce a Jihar Filato. Na yi karatun firamare a makarantar Army Transferred, sannan na shiga ƙaramar sakandire a makarantar da ake kira da At-Tawheed kusa da barikin sojojin sama dake Jos, kafin daga bisani na wuce babbar sakandire a makarantar Al-Iman School. Daga nan na shiga makarantar koyon sarrafa na’urar kwamfiyuta, inda na samu shaidar Diploma. Na samu damar shiga Jami’ar Jos, inda aka bani damar karanta aikin zayyanar gidaje da muhalli a matakin digiri na farko, har na kai shekara ta uku, amma dalilai da dama suka sa dole na nemi canjin layin karatu, domin tunawa da farko ba shi ne karatun da nake so na yi ba. Na sauya layin karatuna na koma sashin nazarin aikin koyarwa da tsara darussan karatu, inda a nan ne na kammala digirina na farko. Akan wannan layin na yi digirina na biyu a wata Jami’a dake ƙasar Malaysiya, yanzu haka kuma na kusa kammala karatun digirina na uku a Jami’ar Abubakar Tafawa ɓalewa dake Bauchi. Na yi kwasa-kwasai da dama, daga cikin akwai karatun da na yi a wata cibiyar horar da malamai ta birnin Landan, inda na samu ƙarin gogewa kan dabarun koyar da Turanci ga waɗanda ba asalin Turawa ba. Yanzu haka kuma ina nazari kan dabarun koyar da ƙananan yara daga haihuwa zuwa shekara shida zuwa takwas.
Yaya ki ka samu karatu a lokacin tasowarki, kin samu wani ƙalubale wajen neman ilimi?
A lokacin da muka taso mun samu goyon bayan iyaye kan sanya mu a makaranta da biya mana kuɗin makaranta, sai dai da yake iyayenmu a wancan lokacin ba zurfin karatu suka yi na boko ba, ba mu samu gatan da yaran yanzu suke samu ba, wanda in yaro ya dawo a gida za a yi masa bita a kuma taya shi aikin gida da ake bayarwa. Amma Alhamdulillah, mun samu damar karatu, an tallafa mana, ba mu samu wata tangarɗa ba. Kodayake an farko na ɗan fuskanci matsalar kasa fahimtar Turanci, saboda makarantar firamare da muka yi ta gwamnati ce, ba a cika ba da muhimmanci ga yin magana da Turanci ba, don haka ko da na shiga sakandire a At-Tawheed inda nan kuma ana bai wa magana da Turanci muhimmanci na ɗan fuskanci ƙalubalen yin magana da Turanci. Amma cikin ikon Allah kafin na kammala aji uku na ƙaramar sakandire sai da ya zama duk wata kyauta da za a bai wa ɗalibi mafi ƙwazo da ƙoƙari, ni nake cinyewa. Dalilin haka kuwa shi ne ina da naci da son sai na san abin da ban sani ba.
Zan so in ji irin yanayin gidan da ki ka taso, yaya yanayin tarbiyyar da ku ka samu a game da ilimi da zamantakewa ta rayuwa?
To, Alhamdulillahi. Gaskiya ni na taso a gidan da ake da tsananin kishin karatu. Mahaifinmu, Allah Ya jiƙansa da rahama, mutum ne mai matuƙar son ganin yaransa sun samu ilimi ingantacce. Ina iya tuna cewa a lokacin muna yara akwai kantin sayar da littattafai musamman da aka keɓe mana nan muke zuwa karɓar takardun makaranta ko abubuwan karatu. Ko da na fara tasowa ina da ƙwaɗayin son karatu, a lokacin na fara gane abin da nake karantawa, musamman mahaifinmu yake sayo min littattafan karatu na gida, don ya ƙara min ƙwarin gwiwa. Sannan akasari makarantun da muka yi suna da tazara sosai da gidan mu, amma haka mahaifinmu yake ɗibanmu a mota ya kai mu makaranta, kuma ya je ya dawo da mu ba tare da latti ko fashi ba. Babu shakka mahaifinmu ya yi wa ilimi hidima sosai. Ina ganin nasarorin da muke samu yanzu a matsayin mu na ‘ya’yansa yana da nasaba da jajircewar da mahaifinmu ya yi a kan cigaban ilimi. Alhamdulillah!
Wanne ɓangare na wannan tarbiyyar da ku ka samu yanzu ke ma ki ke ƙoƙarin koya wa naki yaran?
To, Alhamdulillahi. Kasan zamanin mu da na iyayenmu ba ɗaya ba ne. Su a lokacin su kishin ilimin da hidimtawa ilimin ne a gabansu ba wai don sun yi wani karatun boko mai zurfi ba. Amma mu yanzu mun yi karatun, kuma muna ƙoƙarin ɗora yaranmu a kai, muna karatu tare da su, muna taya su ayyukan makaranta, muna ƙara gogar da su a gida kan abubuwan da aka koya musu a makaranta. Muna ƙoƙarin sauke nauyin dake kanmu a matsayin mu na iyaye, mun sa su a makarantu masu kyau, muna biya musu kuɗin makaranta mai tsada, muna saya musu kayan karatu daidai gwargwado. Wannan yana sa ina tuna jajircewar da iyayenmu suka nuna wajen sanya mu karatu da ɗawainiya da mu. Allah Ya saka musu da alheri.
Ko za ki gaya mana abin da ya sa miki kishin karatu da son koyar da ƙananan yara?
Kamar yadda na faɗa a baya a lokacin ina jami’a an bani damar in karanta ilimin tsara zayyanar gidaje da muhalli ne wato Architecture, amma kuma na canza zuwa ɓangaren koyarwa. Tun a lokacin nake ji a raina lallai akwai buƙatar ba da gudummawa don samar wa yara ilimi mai inganci. Haka na riƙa ji tun a wancan lokacin, sai ina ganin ina da gudummawar da zan iya bayarwa wajen inganta cigaban ilimi. Duk da yake a lokacin akwai ƙuruciya, ba wani girma na yi sosai ba. Sannu a hankali ina cigaba da karatu na fahimci lallai bai wa yara ilimi mai inganci tun a matakin farko, ita ce gaɓa mai muhimmanci. Idan aka samu tangarɗa daga wannan gaɓar to, yaro har girmansa ba zai fahimci ina aka dosa ba a karatu. Shi ya sa na mayar da hankali a kai, domin samar da tushe mai kyau ga yaranmu masu tasowa.
Kina ganin wannan matsalar ce ta sa muke fuskantar ƙalubale a fannin ilimi a arewacin ƙasar nan?
ƙwarai kuwa! Ai wannan gaɓar ita ce tushe kuma ginshiƙin da kowanne ilimi ya ɗoru a kansa. Idan har za mu samu tushe mai inganci to, babu shakka ilimin yaranmu zai inganta. Kamar a ɓangaren mu, akwai ɗakin karatu da nake kula da shi na tunawa da marigayi Haruna ɗanbale a nan Layin ‘Yandoka dake cikin garin Jos, a ƙarƙashin sa mun buɗe sashin rainon ƙananan yara dake da matsalar fahimtar karatu, wanda muke kira da Reading Clinic, muna gogar da su yadda za su iya sanin ƙa’idojin karatu da haruffan Turanci. Wani lokaci zan ka ga an kawo yaro wanda yake aji na uku ko na huɗu, amma bai san ya zai yi ya haɗa baƙi ya yi karatu ba. Saboda rashin samun tushe mai kyau daga makarantar da aka sa shi. Daga nan mu kuma za mu yi irin namu ƙoƙarin mu yi amfani da dabarun da muke da su, don mu ga ya samu canji sosai a karatunsa.
Waɗanne dalilai ne suka sa ku ka kafa wannan makaranta, kuma shin kwalliya tana biyan kuɗin sabulu?
Na fara tunanin kafa wannan makaranta ne tun daga gidana, a lokacin da na tashi sa yarinya yarinyata a makaranta, ban samu makarantar da ta dace da abin da nake so ba a kusa da inda muke, inda kuma nake tunanin zan samu abin da nake so ba a kusa ba ne. Bilhasali ma ba na musulmi ba ne, kuma suna da tsada sosai. A lokacin kuma mahaifinsu ya nunar min da cewa, ba ya son yaransa su taso a inda babu tarbiyyar addini, don haka ya zama min ƙalubale sosai in samo mafita. A lokacin ma ban fara koyarwa ba, amma na kammala digirina na biyu, na dawo daga Malaysiya, don haka sai na yi tunani me zai hana ni na fara koya mata bisa tsarin da nake so, tun da abin da na karanta kenan. To, a gaskiya da ita na fara, mijina ya bani goyon baya na ware ɗaki guda a cikin gidanmu na mayar da shi aji, muka fara karatu. Sannu a hankali har yaran maƙwafta ma suka fara shigowa, ana koyar da su. A lokacin da aka samu annobar cutar Korona, sai abin ya daɗa bunƙasa, har ma ya fi ƙarfin ɗakin da muke amfani da shi, muka koma amfani da wani sashi na gidan.
To, kamar yadda yake bisa ƙa’idar irin wannan koyarwa, akwai matakin da za a kai dole a samar wa yara littattafan da za su riƙa karatu da shi, suna gane cigaban da suke samu. Wannan shi ne ya haifar da ɗakin karatu da yanzu muke amfani da shi, bisa amincewa da goyon bayan maigidana, Farfesa Balarabe Yusha’u, wanda ya sa wa wajen sunan kakansa, marigayi Haruna ɗanbale. Mun fitar da litattafai bisa manhajar da muka tsara wanda na tattaro daga namu na gida da kuma na wasu ƙasashen Turai da na samu daga wajen ƴan’uwata dake karatu a can. Kuma yanzu haka dubban ɗalibai ne suke amfana da su. Kuma babu abin da muke samu daga iyaye sai addu’a da sa albarka, domin suna ganin sakamakon abin da muke koyawa yaransu, daga nasarorin da suke samu a makarantun da suke zuwa.
A matsayinki ta malama kuma mai kishin ilimi, yaya kike kallon ƙalubalen da harkar ilimi ke fuskanta a arewacin ƙasar nan?
Za mu samar da amsar wannan tambayar a mako mai zuwa idan Allah Ya amince. Kafin wasu tambayoyin su biyo baya.
