Ƙorafe-ƙorafe guda shida aka gabatar wa kwamitin zaɓen shugabannin APC a Katsina, inji shugaba

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An bayyana cewa, ƙorafe-ƙorafe guda shida aka shigar gaban kwamitin kula da ƙorafi na zaɓen sababbin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Katsina.

Shugaban kwamitin sauraren ƙorafe ƙorafe na zaɓen da ya gudana na shugabannin jam’iyar APC a matakin gunduma a jihar Sadiq Mohammed Ali ya faɗawa manema labarai a Katsina.

Wasu ya’yan jam’iyar ne suka gabatarwa kwamitin da waɗannan ƙorafe ƙorafe na nuna rashin gamsuwa da yadda a ka gudanar da zaɓen a yankunansu.

Ya bayyana cewa kwamitin ya zauna da waɗannan mutane ya kuma saurari koken inda ya yace kwamiti ya zauna akan su kuma zai miƙa rahoton su ga kwamitin zartarwa ta ƙasa.

Sadiq ya sanar da cewa kwamitin sa ya gudanar da zaɓen shugabancin jam’iyar a matakin gunduma 361 da na ƙananan hukumomi 34 waɗanda aka bi ta hanyar sasanci.

Haka kuma a cewar sa kwamitin ya bi tsarin mulki da ƙa’idojin jam’iyar su ta APC wajen gudanar da zaɓukan.

“Ina tabbatar maku da cewa munbi ƙa’idojin da tsarin mulkin da jami’ya ta shimfida wajen gudanar da zaɓen”Sadiq ya ce.

Shugaban kwamitin ya bayyana cewa sun gama zama akan ƙorafe ƙorafen wanda yanzu haka a cewarsu sun kammala rahoton su da za su gabatar wa kwamitin zartarwa ta ƙasa.

Duk wani ƙorafi da aka gabatar a gaban kwamitin ya ce ta ɗauka da mahimmanci kuma za a sami daidaito.

Dangane da zaɓen shugabannin jam’iyar na ƙananan hukumomi da shima ya gudana Sadiq Mohammed ya bayyana cewa har yanzu kwamitin na amsar ƙorafe ƙorafe wanda yayi kira ga waɗanda ke da korafi su kawo kwamitin a rubuce.

Ya yabawa kwamitin shirya zaɓen ƙarƙashin jagorancin shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin Katsina Hon Abdulkadir Nasir Andaje da yace ba su da matsala dan kan kwamiti su ba.

Tunda farko shugaban kwamitin da ya gudanar da zaɓen Yakubu Bashir Bello ya bayyana cewa an samu nasarar gudanar da zaɓen a jihar domin mutane da dama sun fito sun shaida yadda aka gudanar da zaɓen.

Ya ce kusan ko ina sun gudanar da sasanci kamar yadda uwar jam’iyar APC ta ƙasa da masu ruwa da tsaki na jam’iyar suka aminta da haka.

By ukarofi