Daga JOHN D. WADA a Lafia
Wani mataimakin shugaban al’ummar Koro na shiyar Keffi da Karu a jihar Nasarawa mai suna Ɗanladi Adukwa ya yi kira na musamman ga gwamnatin jihar Nasarawa da ta tarayya da shugabanni da hukumomi da suka dace da masu fafutikar kare hakin ɗan Adam musamman fannin shari’a da su hanzarta kawo masu ɗauki sakamakon ƙwace masu dukiyoyinsu da ke ƙauyen Kunduro-Bakin kogi a yankin Rayawa na Pandam na ƙaramar hukumar Karu jihar Nasarawa. Inda suka ce wasu da suka fi ƙarfin su ke cigaba da ƙwace masu filaye a yankin.
Ɗanladi Adukwa ya bayyana alhinin sa ne a madadin ‘yan uwansa al’ummar Koro na yankin baki ɗaya lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ƙauyen.
Yace sun tashi sun ga iyayensu Kwarawan suna zama a wajen shekaru aru-aru basu taba samun labarin cewa waɗannan filayensu na noma da sauran su na wasu daban bane sai a yanzu.
A cewar Ɗanladi Adukwa hakan ya basu mamaki tare da tayar masu da hankali don galibin ‘yan uwan nasa da ke ƙauyen manoma ne da suka dogara da aikin noman don ciyar da iyalansu da biyan buƙatun rayuwansu na yau da kullum, amma a yanzu haka abinda ke faruwa shine a duk lokaci da suka tafi gonakinsu sai su ga an yi gini an sa bicon an kewaye musu filayen sannan su ga wasu mutane daban su rika korar su cewa an riga an sayar da gonakin.
Ɗanladi Adukwa ya cigaba da bayyana cewa” Ana haka ne muka ce bamu yarda ba sai hakimin yankin Kunduro-Yaskwa mai suna Sabo Abu wanda ke cigaba da sayar mana da filayen kenan ya kai ƙarar mu kotu sai mu kuma muka samu namu lauya amma duk da muna kotu da shi hakimin ana shari’a sai ka ga an sake kamo wani daban wanda ya sake sayar masa da filinmu.
Yanzu ma akwai wata mata hajiya wacce itama ta sayi kimanin hecta 280 na gonakin namu gun hakimin da wani kuma wai shi sarki mai sanda da Timothy da dai sauran su da yawa duk sun saya daga hakimin inji su.”
Danladi Adukwa ya ƙara da cewa ba a tsaya ban ba a yanzu an kawo wasu Fulani ne da suma wai ana sayar musu da gonakin kuma a yanzu haka filayen gonakin sun kusa kare da hakan yasa a yanzu al’ummar nasu na Koro a yankin sun rasa komai basu da wani abun yi sakamokon zaluncin.
Daga nan sai mataimakin shugaban al’ummar Koro na shiyar Keffi da Karu, Danladi Adukwa ya nanata kukansu ga gwamnatin jihar ta Nasarawa da hukumomi da suka dace ciki har da kotun da ke saurarar ƙarar su sa baki a maganar don maganar yafi karfin su don duk da maganar na kotun sama da shekaru 13 kenan amma har yanzu hakimin na cigaba da yin amfani da ƙarfi yana sayar musu da filayensu ba gaira ba dalili kuma a yanzu da za a fara aikin noma al’ummarsa Kwarawar yankin basu san yadda zasu yi ba kuma waɗanda ke noman rani suna zaune a gida yanzu babu aiki don an karɓe musu gonakin su.
Suma da suke bayyana wa ‘yan jarida kukan nasu wasu magabata daga cikin Kwarawar da lamarin ya shafa da suka haɗa da Dauda Alhassan da Baba Danjuma Philips da sauran su duk sun tabbatar da jawabin wanda yayi magana a madadin su inda suma suka buƙaci gwamnatoci a duka matakai da hukumomi daban-daban da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam su taimaka su kawo musu ɗauki a lamarin su kuma samar musu da jami’an tsoro a yankin don a yanzu haka rayuwansu na cikin hatsari don duk wanda ke ƙwace maka dukiya tabbas zai iya halaka ka, inji su.
A ƙarshe duk ƙoƙarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin waɗanda ake zargi da ƙwace tare da sayar da filayen musamman shi hakimi Sabo Abu ya ci tura don bai samu ganinsa ba a yayin haɗa wannan rahoto.
