Gobarar Los Angeles: Hollywood ta shiga muhawara kan bikin Oscar na bana

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Yayin da gobarar daji ke ci gaba da mamaya a birnin Los Angeles, a karon farko cikin shekaru goma, bikin Oscar ya shiga a babin ƙila-wa-ƙala, yayin da masana’antar Hollywood ta dasa alamar tambaya kan, ko ya kamata a gudanar da taron na bana? Idan kuma amsar e ce, to me ake nufi da yin hakan a yanzu?

Girman ɓarnar da aka yi a Kudancin Kalifoniya ya yi tasirin da ya kawo tazgaro ga manyan shagulgulan bukukuwan shekara-shekara da suke da tarihi a masana’antar fim, wanda hakan ya faru cikin ƙanƙanin lokaci. 

Lokacin da gobarar Palisades ta tashi, lokacin bayar da lambobin yabo na Hollywood yana kan ci gaba. The Golden Globes ya faru ƙasa da sa’o’i 48 da suka gabata kuma jerin lambobin yabo masu ban sha’awa da suka biyo baya a cikin kwanaki bayan.

Gobarar ta mamaye tsakiya, kuma zuciyar masana’antar finafinan Hollywood, wanda har zuwa yanzu tana ƙoƙarin ganin ta daidaita, duk da dai ba za a iya cewa, wannan ce kawai matsalar da masana’antar ta taɓa fuskanta ba, duba da irin faɗi-tashi da ƙalubalen da ta fuskanta na tsayin shekaru daga matsaloli irin su, hargitsin ma’aikata, sauyawar fasaha da sauransu. 

“Tare da girmamawa na ke roƙo, a lokacin bikin karramawa na Hollywood, Ina fata kowacce kafar sadarwar na talabijin da masu ɗaukar nauyin yaɗa bikin karramawa da masu ɗaukar nauyin shirin, za su watsar da su a wannan karon, a maimakon haka, su sauya akalan kuɗaɗen da suke kashewa wurin bayar da gudunmawar ga waɗanda gobarar ta shafa da kuma masu kashe gobarar,” jarumi Jean Smart, wanda ya lashe Globe kwanan nan, ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Oscar zai iya ci gaba da kasancewa kamar yadda aka tsara, amma akwai tabbacin cewa, za a samu babban sauyi albarkacin gobarar dajin, kuma mafi yawa daga cikin shagulgulan da aka saba za su samu taka birki, duba da cewa, gobarar ta bar mutane da yawa ba tare da gida ba, sanadiyar ƙonewa ƙurmus da gijajen shahararru da masu ruwa da tsaki na masana’antar suka yi.

Dogon nazari aka shiga don ganin an yanke hukuncin da ya fi dacewa, shin me bikin na Oscar zai nuna ga halin da birnin Los Angeles yake ciki. Wasu na ganin rashin dacewar gudanar da shi, yayin da wasu ke ganin zai iya zama haske na ƙarshen kogo mai duhu da mutanen birnin suka shiga, kuma da yiwar bikin na Oscar ya zama matsayin fitilar juriya ga duk wani da iftila’in ya shafa.

Jan ƙafar da ake yi na gudanar da al’adun farko kafin bikin zai iya lurar da yadda ake muhawara kan yi ko barin shi, domin a karo na biyu, Makarantar Koyar da Finafinai a ranar Litinin da ta gabata, ta sake jinkirta sanar da sunayen waɗanda a cikinsu za a zaɓi waɗanda za a ba wa kambu na Oscar a ɓangarori daban-daban. A maimakon haka, an sanar da ɗage fitar da sunayen har zuwa watan gobe, wato ranar 23 ga watan Fabrairu. Cibiyar ta kuma soke liyafar cin abincin rana da ake gudanarwa na shekara-shekara kuma ta ce tana shirin karrama ma’aikatan sahun gaba a kwantar da gobarar da kuma gabatar da tallafi na rage raɗaɗi kan halin da aka shiga.

“Za mu shawo kan wannan, kuma za mu take, tare da samar da hanyoyin waraka ga al’ummar finafinanmu na duniya,” inji Bill Kramer, shugaban Makarantar Fim, da Janet Yang.

Gobarar, ɗaya ce daga cikin bala’o’i mafi tsada a tarihin Amurka, wadda har izuwa yanzu tana  ci gaba da ruruwa tare da laƙumi rayuka da dukiyoyi, wanda ya zuwa yanzu ta yi sanadiyar mutuwar mutane aƙalla 25. Wannan ne ya sake tsare-tsaren gudanar da bukukuwan na al’ada a Hollywood. Daga ciki kuwa akwai ɗage bayar da lambar yabo ta Critics Choice Awards.

An jinkirta fitar da sunaye na Producers Guild Awards sau biyu ba tare da wata sabuwar rana ba.  Kuma a ranar Talata, ƙungiyar ta kafa gidauniya don tallafa wa furodusoshin su da gobarar ta shafa.

Kyautar Grammy karo na 67, da aka shirya gudanar da shi a ranar 2 ga Fabrairu a cikin garin Los Angeles, na nan bai canza ba, duk da cewa an samu manyan canje-canje. Harɓey Mason jr., Babban Jami’in kula da naɗe murya na makarantar, kuma Shugaban Kwamitin Amintattu Tammy Hurt ya ce, Grammys na wannan shekara “zai kasance kamar yadda aka shirya, saidai an samu sauye-sauye da dama, domin zai mayar da hankali kan tara kuɗaɗe don tallafa wa ɓangaren da gobarar ta shafa, tare kuma da karrama jajirtattun da suka sadaukar da rayukansu wurin ganin sun ba mu kariya.”

Dangane da yadda gobarar ta taɓa masana’antar finafinai ta Hollywood kuwa, Cibiyar masu shirya finafinai ta samu kasonta a iftila’in, inda gobarar ta laƙume gidajen mutane huɗu daga cikin ‘yan kwamitin zartarwa 55 na makarantar, a cewar The Hollywood Reporter, ciki har da furodusa Lynette Howell Taylor, gwamnan ingancin Brooke Breton, gwamnan reshen sauti Mark P. Stoeckinger da gwamnan reshen animation Jinko Gotoh.

Palisades na Pacific, wanda gobarar ta lalata da yawa, ta kasance gida ga taurari da shuwagabanni da yawa.

Isabella Rossellini, wacce sunata ke cikin jerin waɗanda za a zaɓa a matsayin jarumar da ta fi bayar da tallafi saboda rawar da ta yi a cikin ‘Conclaɓe”, a Instagram ta sanya hoton Oscar da ke nuni da muna tsimayen zuwan ranar.

An tilastawa wasu manyan gidajen talabijin da yawa dakatar da yaɗa rahotannin da suka shafi gobarar, musamman ma na ƴan fim cin da iftila’in ya shafa.

Har zuwa yau aiki a cikin masana’antar finafinai da kuma ɓangaren talabijin bai dawo daidai ba biyo bayan yajin aikin da aka gudanar a shekarar 2023, wanda ya yi sanadiyar rasa aikin yi ga masu aikn yin fim, sanadiyar fasahar zamani da ke mamaye guraben ayyukansu. Don haka sutudiyo da dama za ka ji shi shiru, sakamakon na’ura ce ke aikin da a baya mutane da dama ke yi. Wannan ne ya sa a yayin wannan gobarar, jarumar fitaccen fin ɗin nan mai dogon zango da ya kafa tarihi a ilimantarwa kan sha’anin harkar lafiya cikin nishaɗi, Grey’s Anatomy, wato Natalie Morales, ta bayar da shawarar mayar da sutudiyo-sutudiyon da ake da su ajujuwan karatun yara na wucin gadi, ga yaran da makarantunsu suka ƙone, kasancewar an ginasu tun a zamanin da mutane ke iya cika su don yin aiki, wato ma’aikata. 

By ukarofi