Buhari ya halarci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya kira taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Katsina akan zaɓen ƙananan hukumomi da ke tafe a cikin wata mai zuwa.

Taron da ya gudana a gidan Gwamnatin jihar ya sami halartar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da tsofaffin gwamnoni guda uku.

Akwai Rt Hon Aminu Bello Masari,Barista Ibrahim Shehu Shema da tsohon gwamnan soja Rtd colonel Abdulmummuni Aminu.

Haka kuma akwai mataimakin gwamnan jihar Katsina Malam Farouk Lawal Joɓe da mai ba shugaban ƙasa shawara akan harkokin siyasa Kabir Ibrahim Masari.

Sai ministan gidaje Arch Musa Ɗangiwa da ministan al’adu Hajiya Hannatu Musa Musawa da tsohon mataimakin gwamnan jihar Katsina Barista Surajo Umar Samari.

Akwai jigo a jam’iyar APC a jihar Alhaji Ɗahiru Barau Mangal da tsafin ƴan majalisar dokoki ta ƙasa na da dana yanzu.

A jawabin sa gwamna Dikko Raɗɗa ya yi kira ga ya’yan jam’iyyar APC a jihar masu riƙe da muƙami a gwamnati da su taimaka wa jam’iyyar a mazaɓarsu domin samun nasarar zaɓen ƙananan hukumomi mai zuwa.

Yayi godiya ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu kan manyan muƙamai da suka ba ya’yan jihar.

A nasa jawabin mataimakin gwamnan jihar Farouk Lawal Joɓe ya bayyana aikace aikace na bunƙasa ƙasa da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta aiwatar a jihar.

Ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan tara na sayen kayan masarufi domin azumin watan Ramadan mai zuwa.

Za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin ne a cikin wata mai zuwa a jihar.

By ukarofi