Daga AISHA ASAS
Likita ya ba wa jarumi a masana’antar finafinai ta Indiya, wato Bollywood, Saif Ali Khan sallama daga asibitin Lilaɓati da ke birnin Mumbai kwanaki biyar bayan an caka masa wuka, inji kamfanin dillancin labarai na PTI.
Rahoton ya rawaito cewa, jaruma Kareena Kapoor, kuma mata ga jarumin ce ta ɗauko maigidan nata daga asibiti.
Manhaja ta ruwaito dlilin kwamciyar jarumin asibiti a makon da ya gaba, inda a safiyar ranar Alhamis ne wani mutum ya shiga gidan Saif Ali Khan da ke Bandra inda ya caccaka masa wuka a wurare da dama, lamarin da ya sa ya samu munanan raunuka.
Saif Ali Khan ya ji rauni a wurare shida a wannan harin, ciki har da raunuka masu zurfi a ƙashin bayansa da wuyansa. Likitoci sun ce “An cire wuka mai tsayin inci biyu da rabi daga ƙashin bayansa,” kamar yadda rahoton BBC Hausa ya tabbata.
Daga baya, ƴan sandan Mumbai sun kama wani mutumin da ake zargi da kai harin. Mataimakin kwamishinan ƴansandan shiyyar Mumbai-9, Diɗit Gedam ya bayar da bayanai game da maharin mai suna Mohammad Shariful Islam Shahzad mai kimanin shekara 30, wanda ya shiga gidan Saif da nufin yin sata. Kuma an samu nasarar damƙe shi ne a Hiramandi Labor Camp da ke Thane
