Gombe JAAC ta gargaɗi ƙananan hukumomi kan almubazzarancin kuɗi

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Kwamishinan ma’aikatar ƙananan hukumomi da bunƙasa al’umma ta Jihar Gombe, Barr. Sani Ahmed Haruna (Wakilin Arewa Gombe), ya gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi 11 da kuma Local Council Development Areas (LCDAs) da su guji almubazzarancin kuɗaɗen jama’a.

Haruna ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da yake jagorantar taron kwamitin hadin gwiwa na asusun ƙananan hukumomi (JAAC) na watan Satumba na shekarar 2026, wanda aka gudanar a ɗakin taro na ma’aikatar.

Ya umurci shugabannin ƙananan hukumomin da su mayar da hankali wajen aiwatar da ayyukan da za su magance buƙatun al’ummominsu na yau da kullum, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwa da tsaftar muhalli.

Kwamishinan ya ce ingantaccen tafiyar da albarkatun kasa a matakin ƙananan hukumomi na da matuƙar muhimmanci wajen inganta rayuwar jama’a da samar da ci gaba mai ma’ana a cikin al’ummomi.

A yayin taron, daraktan baitulmalin ya gabatar da rahoton kuɗi na watan, wanda ya ƙunshi rabon kuɗaɗe da sauran harkokin kuɗi na ƙananan hukumomi da LCDAs.

Kwamishinan lafiya, Farfesa Adamu Danladi Bojude, ya gabatar da takarda kan shirin bayar da tallafin kiwon lafiya da tiyata kyauta na shekarar 2026, kashi na biyu.

Bojude ya ce shirin zai samar da ayyukan kiwon lafiya da tiyata kyauta ga mazauna jihar, musamman waɗanda ke zaune a yankunan da ke da ƙarancin cibiyoyin kiwon lafiya.

Ya kuma gabatar da jadawalin shirin tallafin kiwon lafiya na shekarar 2027, inda ya jaddada buƙatar kai muhimman ayyukan kiwon lafiya kusa da jama’a a matakin karkara.

Shi ma kwamishinan matasa da bunƙasa wasanni, Barr. Yusuf Abdullahi Kwadon, ya yaba wa shugabannin ƙananan hukumomin bisa ayyukan da suke aiwatarwa a yankunansu.

Ya buƙaci shugabannin da su ci gaba da wannan ƙoƙari tare da ƙara zuba jari a shirye-shiryen da za su samar da damammaki ga matasa da kuma bunƙasa ci gaba mai ɗorewa a matakin ƙananan hukumomi.

A nasa ɓangaren, jami’in hukumar jarabawar kasuwanci da fasaha ta ƙasa (NABTEB) na jihar, Malam Abdullah Shuaibu Danbaka, ya yi bayani kan ayyukan hukumar, inda ya buƙaci ƙananan hukumomi da su tallafa wa masu sana’o’i da sauran ƙwararru da abin ya shafa wajen samun takardun shaidar ƙwarewa.

A halin da ake ciki, Babayo Abubakar daga sashen bincike, sa-ido da tantance ayyuka na ma’aikatar, ya gabatar da rahoton ayyukan da aka gudanar a ƙananan hukumomi da LCDAs a watan Agustan 2026.

Rahoton ya nuna cewa sama da kashi 90 cikin 100 na ayyukan da aka sanya ido a kansu an kammala su, yayin da kusan kashi 10 cikin 100 ke ci gaba da gudana.

A fannin ilimi, an aiwatar da ayyuka 25, wadanda suka kai kashi 23.14 cikin 100, yayin da bangaren kiwon lafiya da ruwa da tsaftar muhalli kowannensu ya samu ayyuka 18, wanda ya kai kashi 16.66 cikin 100.

Sashen ya bayar da shawarar ƙara bai wa ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwa da tsaftar muhalli fifiko, yana mai bayyana su a matsayin muhimman fannoni wajen inganta rayuwar jama’a.

Haruna ya yaba wa shugabannin ƙananan hukumomin bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen bunƙasa al’umma, sannan ya buƙace su da su tabbatar da gudanar da kuɗaɗen jama’a cikin tsari da gaskiya tare da kammala ayyukan da ake gudanarwa cikin lokaci.

Taron ya samu halartar shugabannin ƙananan hukumomi da LCDAs, babban sakataren ma’aikatar, daraktoci, daraktan baitulmalin da sauran manyan jami’an gwamnati.

By ukarofi

Leave a Reply