Gwagwarmayar neman shugabancin Majalisar Dokokin Nijeriya ya ɗauki salon addini

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Daga dukkan alamu addini zai taka muhimmiyar rawa a yunƙurin da ake yi na samar da sababbin shugabannin Majalisar Dokokin Nijeriya, wacce ta ƙunshi Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai.

Bayanai sun nuna cewa, wannan ya biyo bayan kasancewar zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa, Alhaji Kashim Shettima, dukkansu Musulmi ne.

Hakan ya sanya wasu ’yan majalisun masu jiran gado ke kurarin cewa, ba za ta saɓu ba a zaɓi Shugaban Majalisar Dattawa Musulmi, har ma wasu ke ganin cewa, hatta Kakakin Majalisar Wakilai shi ma bai dace ya zama Musulmi ba. Wato yadda vangaren zartarwa zai kasance na Musulmi ne zalla, wao Shugaban Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, shi ma ɓangaren Majalisar Dokoki ya kasance Kiristoci ne zalla.

Tuni dai wasu zaɓaɓɓun ’yan majalisa masu jiran rantsuwa suka nuna sha’awarsu ta tsaya wa takarar shugabanci a majalisun dokokin na ƙasa guda biyu, inda aka samu mabiya addinai daban-daban daga cikinsu, duk yadda yaƙin neman zaɓen ke sauya salo zuwa addinanci.

Wasu masu ra’ayin mabiya addinin Kirista su na kallon lamarin a matsayin rashin adalci, musamman ma kan kujerar Shugaban Majalisar Dattawa, wacce idan aka samu Musulmi ya ɗare kanta a 2023, to Nijeriya za ta kasance masu riƙe da manyan muƙamanta uku, wato Shugaban Ƙasa, Mataimakin Shugaban Ƙasa da Shugaban Majalisar Dattawa, dukkanninsu Musulmi ne.

Bugu da ƙari, a halin da ake ciki yanzu, zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Wakilai, wanda ake ganin shine a kan gaba wajen samun goyon bayan masu riqe da madafun iko a neman kujerar Kakakin Majalisar Wakilai, wato Hon. Ahmed Idris Wase, kuma Mataimakin Kakakin Majalisar na yanzu, shi ma Musulmi ne.

Wannan ya sake zafafa siyasar ƙasar, inda wasu mabiya addinin Kirista har ma da wasu Musulmin ke ganin cewa, bai dace a bari hakan ta faru ba ko kaɗan.

Amma sai dai masu goyon bayan a yi hakan na da ra’ayin cewa, tsarin dimukraɗiyya ya bayar da fifiko ne kan mafi rinjaye. Don haka, idan har mafi rinjayen ’yan majalisun suka ga dacewar su zaɓi mutum ba tare da la’akari da addininsa ba, to wannan ne dimukraɗiyya ta gaskiya.

A cikin sanatoci masu jiran gado da ake ganin su na neman shugabancin Majalisar Dattawa akwai shi kansa Shugaban Majalisar na yanzu, Ahmad Lawan, da Barau Jibril daga Jihar Kano, Abdulaziz Yari daga Jihar Zamfara, Ali Ndume daga Jihar Borno, waɗanda dukkansu kuma ’yan Arewa ne, inda mabiyansu ke ganin cewa, cikar dimukraɗiyya shine a bai wa kowa ’yancinsa da Kundin Tsarin Mulki ya tanada.

Sai dai kuma akwai Kiristoci daga Kudu, waɗanda su ma suke neman kujerar da suka haɗa da Orji Kalu, Godswill Akpabio, Dave Umahi da Osita Izunaso, waɗanda masu mara musu baya ke ganin cewa, zaman lafiyar siyasar Nijeriya shine a a ɗauki ɗaya daga cikinsu a ba shi kujerar.

Yanzu haka dai gwamnoni, musamman na Jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, su na ta faman zaman ganawa tare da masu ruwa da tsaki, don kwance bakin zaren, musamman ma da ya ke Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya ƙi yarda ya tsoma hannunsa ƙarara a cikin lamarin.