Gwamna Buni zai tallafa wa matasa 300,000 da kayan sana’a don dogaro da kai

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya sanar da ɗaukar matakin taimaka wa matasan jihar 300,000 da tallafin sana’o’i don samun abin dogaro da kai tare da yaƙi da talauci a jihar.

Gwamna Buni ya bayyana hakan ne a lokacin da al’ummar jihar suka shirya masa gagarumar tarba a babban filin wasa na 27 August Stadium, domin taya shi murnar kammala babban taron jam’iyyar APC a matsayin sa na shugaban riqo kimanin shekaru biyu.

A hannu guda kuma, Gwamna Buni ya sha alwashin tallafa wa matasa a faɗin jihar da Keke Napep don inganta rayuwar su domin samun sana’o’in dogaro da kai.

“Waxannan dandazon dubban matasan waɗanda su ne suka fi yawa a cikin al’ummar mu ta jihar Yobe sannan a matsayin su na manyan gobe, wanda bisa ga wannan ne gwamnatinmu ta ƙudiri aniyar bunƙasa rayuwarsu wajen cin gajiyar rayuwarsu da kuma samun aikin yi.”

Bugu da ƙari kuma, Gwamna Buni ya ce ya sadaukar da nasarorin da ya samu a shugabancin riƙon ƙwaryar jam’iyyar APC ga ɗaukacin al’ummar jihar waɗanda suka tsayu wajen yi masa addu’o’i da goyon baya.

A hannu guda, Gwamna Buni ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga yan siyasa a jihar su kasance nagari, tare da bayyana cewa marowatan yan siyasa basu da gurbin zama a gwamnatin sa.

A nashi ɓangaren, Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi zaɓen da ya dace wajen damƙa ragamar jam’iyyar APC a hannun Gwamna Buni, jajirtaccen shugaban da ya jagoranci APC zuwa ga ɗimbin nasarorin da suka haɗa da ƙoƙari wajen haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar.

“A matsayin mu na al’ummar Yobe mu na alfahari da kai, saboda yadda ka yi namijin ƙoƙari fiye da abin da muke tsammani,” ya nanata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *