Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya kai ziyara a cibiyar hada kekunan lantarki guda 500 masu amfani da hasken rana (Keke EVs) ta gwamnatin jihar da ke Katsina, inda aka yi gagarumin shiri na nufin sauya tsarin sufurin birane tare da samar da damammakin tattalin arziki masu ɗorewa ga al’ummar jihar.
A yayin ziyarar duba aikin, mai bai wa gwamna shawara na musamman kan wutar lantarki da makamashi, Dakta Hafiz Ibrahim Ahmed, ya zagaya da gwamnan a cibiyar, inda ya yi masa cikakken bayani kan matsayin aiwatar da aikin, ciki har da yadda ake haɗa kekunan a halin yanzu da kuma shirye-shiryen horas da ma’aikata.
Ya bayyana wa gwamnan cewa a halin yanzu ana ci gaba da haɗa kaso na farko na kekunan lantarki guda 200 a cikin Jihar Katsina, lamarin da ke nuna wani babban ci gaba a kokarin jihar na rungumar sufuri mai tsafta, rage dogaro da man fetur da sauran makamashin da ke gurɓata muhalli, tare da ɗaukar hanyoyin sufuri masu kare muhalli da suka dace da ƙoƙarin duniya na yaƙi da sauyin yanayi.
Baya ga samar da sufuri mai sauki kuma mai inganci, an tsara wannan shiri ne domin ƙarfafa matasa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida.
Zuwa yanzu, shirin ya samu nasarar horas da rukuni biyu na matasa daga ƙananan hukumomi daban-daban na jihar, inda aka basu horo na aikace kan fasahar motocin lantarki, haɗa su, gyaransu da kuma sauran fasahohin da suka shafi makamashi mai sabuntawa.
Waɗannan matasa da aka horas suna taka muhimmiyar rawa a aikin haɗa kekunan lantarkin, wanda hakan ya samar da wani tsari na musamman da ke haɗa koyon fasaha, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa ƙwarewar masana’antu.
Ana sa ran cewa wannan aiki zai samar da ɗimbin guraben ayyukan yi, ya bunƙasa harkokin tattalin arzikin cikin gida, tare da sanya Jihar Katsina cikin sahun gaba a tsakanin jihohin ƙasar nan wajen amfani da fasahohin makamashi mai tsafta da hanyoyin sufuri masu kare muhalli.
Ana aiwatar da wannan shiri ne karkashin kulawar mai bai wa gwamna shawara na musamman kan wutar lantarki da makamashi, a matsayin wani ɓangare na manufofin gwamnatin Raɗɗa na bunƙasa ci gaba mai ɗorewa, ƙarfafa amfani da ƙwarewar cikin gida da kuma bai wa matasa ilimin fasaha da zai taimaka musu a nan gaba.
