Gwamna Raɗɗa ya nemi ƙarin haɗin kai da malaman addini domin magance matsalar ‘yan bindiga

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya yi kira ga malaman addinin Musulunci da su ƙara haɗa kai da jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma domin ƙarfafa yaƙi da matsalar ‘yan bindiga da sauran laifuffuka a faɗin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani shirin wayar da kai da kuma gabatar da muƙala da ƙungiyar Katsina Scholars Forum for Community Advancement ta shirya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Munir Adam Koza.

Gwamna Raɗɗa ya ce magance matsalar tsaro ba zai yiwu ba sai da haɗin kan kowa da kowa, musamman malaman addini, saboda irin tasirin da kalamansu da shawarwarinsu ke da shi a tsakanin al’umma.

Ya ce, “Gwamnati na da alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, amma ita ma al’umma na da alhakin tallafa wa wannan ƙoƙari. Dole ne mu haɗa kai wajen tona asirin masu bai wa miyagu bayanai, kayan aiki da sauran tallafin da ke taimaka musu wajen aikata laifuka.”

Gwamnan ya tuna cewa da ya karɓi mulki, ƙananan hukumomi 23 cikin 34 na jihar sun kasance cikin mawuyacin hali sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ɗauki matakin ɗaukar ma’aikatan Katsina Community Watch Corps guda 2,500 tare da samar musu da kayan aikin da za su tallafa wa ‘yan sanda, sojoji da sauran jami’an tsaro.

A cewarsa, wannan mataki ya haifar da gagarumar nasara, inda hanyoyi da dama da a baya ba su da aminci suka koma cikin kwanciyar hankali, yayin da kasuwanni da dama da aka rufe saboda hare-haren ‘yan bindiga suka koma gudanar da harkokinsu kamar yadda aka saba.

Ya ƙara da cewa duk da cewa mafi yawan ƙananan hukumomin da suka fi fama da matsalar tsaro sun samu zaman lafiya, jami’an tsaro na ci gaba da sanya ido kan sabbin barazanar da ke bayyana a wasu sassan ƙananan hukumomin Musawa da Matazu.

Gwamna Raɗɗa ya yaba da irin gudunmawar da Community Watch Corps ke bayarwa wajen tallafa wa ayyukan tsaro a jihar.
Ya ce, “Allah kaɗai ne ya san irin halin da jihar za ta shiga da ba don gudunmawar Community Watch Corps ba. Sun tsaya tsayin daka tare da jami’an tsaro wajen kare al’ummominmu.”

Har ila yau, gwamnan ya nuna damuwarsa kan masu ba da bayanai da sauran masu haɗa kai da ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Da yake tunawa da sace marigayi Janar Abubakar Rabe, Gwamna Raɗɗa ya ce wannan lamari ya nuna cewa ba za a iya kawo ƙarshen rashin tsaro ba tare da hukunta masu taimaka wa miyagu a ɓoye ba.

Ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa da su guji mayar da matsalar tsaro abin siyasa, tare da buƙatar al’umma su fifita muradun jihar fiye da son rai ko anfani na siyasa.

Gwamnan ya kuma roƙi malaman addinin Musulunci da su ci gaba da yin wa’azi cikin gaskiya da riƙon amana, tare da ƙarfafa mutane su mutunta doka, su ba jami’an tsaro haɗin kai, kuma su inganta zaman lafiya da fahimtar juna.

Haka kuma, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ƙarfafa martaba da walwalar sarakunan gargajiya, musamman Hakimai da Masu Unguwanni, yana mai bayyana su a matsayin manyan abokan hulɗa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

A nasa jawabin, mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Joɓe, ya ce gwamnatin Malam Dikko Umaru Raɗɗa ta ƙarfafa tsarin tsaro ta hanyar inganta walwalar shugabannin gargajiya.

By ukarofi

Leave a Reply