Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan ya amince da hakan ne lokacin da tawagar likitoci daga ƙasar Masar “Egypt” suka kawo mashi ziyarar ban kwana, bayan sun duba wuraren da ake shirin gina cibiyar lafiya ta zamani a jihar Katsina.
Tawagar ta yaba da jajircewar gwamnatin jihar wajen inganta kiwon lafiya, musamman shirin gina cibiyar kula da cutar daji da sauran fannoni na musamman.
Likitocin kuma sun bada shawarar a samar da cibiyar a tsohon ginin Katsina City Mall, kuma gwamnan ya amince .
Gwamna Raɗɗa ya tabbatar da shirin sa na haɗin gwiwa da likitocin don tabbatar da wannan muhimmin aiki, wanda zai rage fita ƙasashen waje neman magani, tare da jawo marasa lafiya daga jihohin ƙasar nan zuwa Katsina
