Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da bada fifiko ga inganta tsaro da fannin noma da sauran fannoni daban-daban a jihar don cimma burin gwamnatin nasa na kiyaye dukiyoyin al’umma da rayukansu tare da da gudanar da shugabanci nagari a koyaushe.
Gwamnan ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen taron raba wasu sabbin motoci da babura da daraktoci wa hukumomin tsaro dabandaban da sauran hukumomin gwamnatin sa wadda aka gudanar ranar Laraba na mako da ake ciki a gidan gwamnati dake Lafiya fadar jihar.
Ya ce tunda ya hau karagar mulkin jihar a matsayin gwamnan jihar a shekarar 2019 ya yanke shawarar yin duka mai yuwa wajen cika alkawarin rantsuwar da ya dauka na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar baki ɗaya tareda samar musu da ribobin dimokaradiya akoyaushe.
Ya ce tabbas idan akayi la’akari da mahimmancin tsaro da sauran fannonin rayuwa a jihar dole ne gwamnatinsa ta cigaba da ire-iren tallafin don inganta harkokin wadannan hukumomi musamman na tsaro a fadin jihar baki daya.
Gwamna Abdullahi Sule ya kuma yaba wa shugabannin hukumomin tsaron da sauran mukarraban gwamnatin sa dangane da cikakken gudumawa da goyon baya da suke bai wa gwamnatin sa musamman ta yin aiki tare da gwamnatin sa inda yace duka dinbin nasarori da gwamnatin sa ta samu kawo yanzu a jihar sakamakon kyakkyawar dangantaka dake tsakanin ta da hukumomin ne.
Daga nan sai gwamnan ya buƙaci hukumomin da suka amfana da ababen hawan su tabbatar sun yi amfani dashi yadda yakamata don akarshe a iya cimma burin gwamnatin nasa a ɓangaren.
Shi ma da yake jawabi tun farko sakataren gwamnatin jihar Ahmed Ubandoma bayan ya jinjina wa Gwamna Sule game da karamcin wanda ya ce tabbas zai je nesa ba kusa ba wajen rage ko kawo karshen ayukan ta’asa da yunwa a jihar ya kuma bukaci wadanda aka basu agajin suyi amfani da su yadda ya dace don kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Abubuwa da aka gudanar a wajen taron raba ababen hawan sun haɗa da gabatar da su wa hukumomin daban-daban da suka haɗa da fannin noma da tsaro da yadda labarai da sufuri da masarautu da dai sauransu.
