Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano
Farfesa Abdullahi Asiru, Shugaban Kwalejin Ilimi da Karatu mai Zurfi ta Gwamnatin Jihar Kano GHACEAS (Ghari College of Education and Adɓance Student Kano) da ke ƙaramar Hukumar Ghari Jihar Kano, ya bayana cewa yanzu haka Gwamnan Jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umarci hukumar gudanarwar makarantar da ta raba fom wato takardar shiga makarantar kwalejin 2000 wanda farashinsa ya kai Naira 5000 kowanne fom kyauta domin dai amfanin matasa da al’ummar Kano da ke da sha’awar shiga makarantun Jihar Kano musamam matasa domin a taimaka musu su yi karatu daidai da manufar gwamnatin Kano a manufofinta na bunƙasa ilimi kamar yadda ta ware kashi 31 cikin 100 a kasafin kuɗinta na 2024 2025 na shekara mai zuwa kamar dai yadda Farfesa Abdullahi ya bayana a hirarsa da manema labarai a Kano a ƙarshen makon da ya gabata.
Haka kuma ya ce yanzu haka wannan kwaleji ta GHACEAS gwamnan kano Abba Kabir, ya farfaɗo da ita an mata gyara ta ko wanne fanni da zai taimaka wajen samar da yanayi na koyo da koyarsa domun kuwa kwalejin yanzu haka akwai wadatacen ruwansha da kayayyakin hasken wutar lantarki da kuma harkar tsaro da sauransu haka kuma a makarantar akwai wuraren kwanan ɗalibai wurin koyo da koyarwa da duk wani da ɗalibi ya ke buƙata kamar harkar sufuri dan zirga-zirga duk kwamna ya yi alwashin wadata makarantar da duk wani abu da ta ke buƙata kuma yanzu haka hukumar makarantar ta karbi mota biyu daga gwamnatin kano a matsayin summon tabi domun yin karatu cikin sauƙi a wannan kwaleji da ke karamar hukumar Ghari Jahar Kano.
Har ila yau ya ce daga cikin karatuntuka ko kwasa kwasai da makarantar zata cigaba da koyar da ɗalibai akwai fannoni daban daban kamar koyar da ilimin sana’a ilimin kasuwanci ilimin noma ilimun tatalin gida wannan duk a sashen ilimun koyar da sana’a kenan sai kuma sashen koyar da ɗaukacin ilimi, ƙarƙashin wannan akwai ilimin manya, ilimun koyarwa a firamare, sai kuma sashen harsuna wanda ya haɗa da sausa da turanci sai addini da Arabiya hausa da nazarin rayuwar dan adam sai kuma sashen koyar da ilimin kimiyya wanda ya haɗa da kimiyya da ilimin halitu kwamfiyuta da ilimun halitu lissafi da ilimun gwamfiyota sai kimiyya da ilimin sani da haɗa sinadarai.
A ƙarshe ya nemi al’umma ta bada haɗin kai da kuma adua domin cigaban kano da al`ummar ta da kuma samun nasara ga gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Jihar Kano.
