Gwamna Tambuwal ya yaba wa Shugaba Buhari bisa kawo ƙarshen matsalar tsaro

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yaba wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bisa ƙoƙarinsa na haɗa guiwa da jihohin ƙasar nan domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan.

Gwamna Tambuwal, wanda shine shugaban dandalin gwamnonin ƙasar nan, haka ma ya jinjina wa rundunar sojin ƙasar nan, bisa haɗa guiwa da gwamnonin jihohin ƙasar nan domin yaƙi da wannan matsalar.

Tambuwal ya bayyana hakan ne dai lokacin da ya karvi baƙuncin manyan jami’an soji mahalarta kwas na 45 na kwalejin soji dake Jaji Kaduna suka kai masa ziyarar godiya na zaɓar Sakkwato domin gabatar da lamuransu.

Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa shakka babu ƙasar nan na fuskantar matsalar tsaro, musamman ma dai wasu sassan jihar Sakkwato, inda ya bayyana cewa rundunar sojin ƙasar nan na iyakacin qoqarinsu wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar nan da ma ƙasa baki ɗaya.

A jawabinsa jagoran mahalarta kwas ɗin na 45 Bigediya General Farouk Mijinyawa, ya gode wa Gwamna Tambuwal bisa basu wannan damar, inda ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da kwas ɗin ya ƙunsa, har da ziyarar yankunan ƙasar nan domin horas da mahalarta kwas ɗin dabarun da za su yi amfani da su wajen yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar nan.

Janar Mijinyawa, ya ce sun zaɓi jihar Sakkwato ne, la’akari da irin nasarorin da ya ce tana samu wajen yaƙi da matsalar tsaro.