Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya gargaɗi masu tasiri a kafafen sada zumunta da masu sharhin siyasa da su guji yin kalamai na raini ko tayar da zaune tsaye kan Jagoran Tafiyar Kwankwasiyya na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Gwamnan ya yi wannan gargadi ne a ranar Juma’a yayin raba babura 600 ga masu tasiri a kafafen sada zumunta, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin Kano.
Gwamna Yusuf ya bayyana Sanata Kwankwaso a matsayin jagora da gudummawarsa ga cigaban siyasa da tattalin arziƙin Jihar Kano ke da matuƙar girma, tare da jaddada cewa ya cancanci girmamawa.
Ya yi gargaɗin cewa yin amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa zagi, ƙarya da kalaman ƙiyayya na iya jefa zaman lafiya da haɗin kan jihar cikin haɗari.
Gwamnan ya jaddada cewa ‘yancin faɗar albarkacin baki dole ne a yi shi cikin alhaki, yana mai cewa muhawarar siyasa ya kamata ta ta’allaka ne kan batutuwa da tattaunawa mai ma’ana, ba kai hare-haren mutum ɗaya ba.
Ya buƙaci waɗanda suka amfana da baburan da su ɗauki tallafin a matsayin nauyi na yaɗa gaskiya, zaman lafiya da ingantattun bayanai game da ayyukan gwamnati a faɗin jihar.
Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa an ƙaddamar da shirin ne domin ƙarfafa masu aikin kafafen sada zumunta, tallafa wa wayar da kan jama’a da kuma inganta sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma.
Ya kuma sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da kwanciyar hankali da bunƙasa zaman tare cikin lumana a harkokin siyasa a Jihar Kano.
