Gwamnan Kano ya yi kira ga masu amfani da kafafen sadarwa na zamani da su gudanar da aikin su cikin tsafta

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga masu tasiri a kafafen sada zumunta musamman magoya bayan gwamnatin da ke kan mulki da su tabbatar cewa abubuwan da suke wallafawa na kasancewa cikin alhaki, girmamawa da mutunci, domin ƙarfafa haɗin kai da ci gaban al’umma.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Yusuf ya yi wannan kira ne yayin Shirin tallafa wa masu tasiri a kafafen sadarwa ta hanyar raba Babura wanda ya haɗa mahalarta daga ƙananan hukumomi 44 na jihar, inda aka gudanar da taron a fadar gwamnati, Kano, a ranar Asabar.

“Na yi kira a gare ku da ku kasance masu alhaki, girmamawa da mutunci wajen ƙirƙirar abubuwan da kuke wallafawa.

“Yancin faɗar albarkacin baki dole ne ya kasance ƙarƙashin ƙa’idojin ɗabi’a, ladabi da girmama ra’ayin wasu.”

“Mu yi amfani da kafafen sada zumunta a matsayin kayan aikin haɗin kai,wayar da kai,ci gaba da sauyi mai kyau ba wai don zagi, tayar da ƙiyayya ko rarrabuwar kai ba. Ina kuma kira gare ku da ku sanya Kano a gaba a duk abin da kuke wallafawa.”

Gwamna Yusuf ya jaddada cewa a wannan zamani na fasaha, kafafen sada zumunta sun zama muhimmin dandali na yaɗa bayanai, fafutuka, ƙirƙira da kuma hulɗar tattalin arziƙi.

Ya bayyana cewa an tsara shirin tallafin ne domin ƙarfafa matasa, bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin Jihar Kano.

“Mun yi imani ƙwarai da gaske cewa ƙarfafa al’umma, musamman mata da matasa, shi ne tabbataccen hanyar rage talauci, rashin aikin yi da munanan ɗabi’u,” in ji gwamnan.

Gwamnan ya kuma yi kira ga masu tasirin da su riƙa haskaka manufofin gwamnatin da ke kan mulki musamman ƙudurinta na tabbatar da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziƙi ta hanyar haɗin gwiwa da sauran jihohi da kuma Gwamnatin Tarayya.

A yayin taron, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Ismail Jibril Falgore, da tsohon Mataimakin Gwamna, Farfesa Hafiz Abubakar tare da shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa, Yusuf Imam, duk sun yi kira ga al’ummar jihar da su rungumi zaman lafiya da haɗin kai a tsakaninsu.

By ukarofi