Jami’ar Alƙalam ta karrama Aminu Bello Masari da digirin girmamawa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jami’ar da ta gudanar da bikin yaye ɗailabai guda 1109 ta kuma karrama mataimakin shugaban Jamaatul Nasarul Islam JNI jihar Imo, Malam Ezeh Abdulfatah Chimeaze Emetumah III shima da digirin girmamawa.

A ranar Asabar 24 ga Janairun 2026, Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa PhD, ya halarci taron yaye ɗaliban Jami’ar Al-Qalam Katsina, karo na 17, inda makarantar ta karrama tsohon Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari, da kuma Ezeh Abdulfatah Chimaeze Emetumah na III da digirin digirgir na girmamawa.

A jawabin da ya gabatar a wajen taron, gwamna Raɗɗa ya fara da bayyana manyan nasarorin da gwamnatin sa ta samu musamman a fannin ilimi, inda ya ce fannin ilimi na ɗaya daga cikin abun da gwamnatin ta sanya a gaba, ya ƙara da cewa gwamnatin ta samar da tallafin karatu na biliyoyin kuɗi domin tallafa wa ɗalibai a matakai daban-daban.

Ya kuma ce an fitar da wasu ɗalibai zuwa ƙasashen ƙetare domin koyon likitanci da kuma ilimin zamani na Artificial Intelligence da Biotechnology, Ya ƙara da bayyana cigaban da aka samu a makarantar koyon sana’o’in hannu ta Katsina (KYCV), inda ya ce an samu sahalewar riƙa bayar da shaidar karatu ta NBTE, lamarin da zai ƙara bunƙasa harkar koyon sana’o’in hannu a jihar.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bai wa ilimi muhimmanci a matsayin ginshiƙin ci gaba mai ɗorewa, tare da yin kira ga jami’o’i masu zaman kansu da su haɗa hannu da gwamnati wajen inganta ilimi.

Gwamna Raɗɗa ya sanar da bayar da motoci ƙirar 206 ga ɗaliban da aka yaye wamda sukayi fice a sakamako, tare da ɗaliban da suka zama saraki da sarauniyar karatu a musabaqar Al-qur’ani da makarantar ke gabatarwa duk shekara.

A jwabinsa Shugaban Jami’ar Al-Qalam, Farfesa Nasir Musa Yawuri, ya gabatar da ta’aziyya bisa rasuwar tsohon Shugaban Gudanarwa na jami’ar, Marigayi Alhaji Aminu Alhasan Dantata, Ya kuma yi bayani kan nasarorin da jami’ar ta cimma, inda ya ce za a yaye ɗalibai a matakan digiri na farko, na biyu da na uku, tare da karrama mutane biyu da digirin digirgir na girmamawa.

A jawabin godiya, tsohon gwamnan jihar Katsina kuma shugaban gudanarwa na asusun tallafawa manyan makarantu Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya nuna matuƙar godiya bisa karramawar da aka yi masa, tare da yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa ƙoƙarin da yake yi na bunƙasa ilimi da ci gaban Jihar Katsina.

Ya kuma yabawa hukumar gudanarwa na jami’ar kan tafiyar da ilimin ɗalibai bada tsari da ƙwarewa.

Tsohon gwamnan jihar sai yayi kira ga shugabannin jami’ar da su mai da hankali wajan koya ɗa’ar ɗalibai.

Masari ya kuma jawo hankalin yan siyasa da su rinƙa tafiyar da harkokin siyasar su bisa tsari da su guji hassada da ƙyashi a tsakaninsu.

Ya bada misalin yadda manyan ƙasashen duniya masu gudanar da mulkin dimokraɗiyya suke tafiyar da gwamnati bisa tsari da bin dokokin ƙasa cikin natsuwa.

Taron ya samu halartar kakakin majalissar dokoki ta jihar Katsina Rt.Hon Nasir Yahaya Daura, Mataimakin Shugaban majalissar Hon. Abduljalal Haruna, Babban Jojin jihar Katsina Mai shari’a Musa Ɗanladi, Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, Alh. Sani Zangon Daura, Alh. Bilya Sanda, yan majalisar jiha, yan majalisar zartarwa, da dai sauran su.

By ukarofi