NUJ a Katsina ta lashe kofin ƙwallon ƙafa na SWAN/Dikko Raɗɗa Cup

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wasan wanda NUJ ta samu nasarar zura ƙwallo 1-0 akan abokiyar karawarta ta ƙungiyar malaman lafiya MHWUN ya basu damar lashe kofin.

Kwamishinan harkokin wasanni da cigaban matasa Eng Surajo Yazid Abukur ya miƙa kofin ga ƙungiyar da ta samu nasara.

Da yake jawabi a lokacin taron, kwamishinan ya bayyana cewa Gwamnatin jihar Katsina na ƙoƙari wajen ganin an samar ma matasa abun yi ta ɓangaren wasanni domin su dogara da kansu a faɗin jihar.

Yayi addu’a da fatan alheri ga dukkanin mahalarta musamman ƙungiyar NUJ da suka samu nasara.

Gadan cin wannan kofi shine karo na farko da ƙungiyar marubuta wasanni ta ƙasa reshen jihar Katsina SWAN ta shirya ya gudana a filin wasa na Muhammadu Dikko a Katsina.

Bayan kammala wasan , shugaban ƙungiyar Malam Nasiru Giɗe ya nuna jin daɗin sa kan yadda ƙungiyoyin suka amsa gayyatar ƙungiyar na shiga cikin wannan gasa.

Malam Giɗe ya bada tabbacin cewa zai yi iya kokarin sa wajan faɗaɗa wannan gasa ya zuwa sauran ƙungiyoyin na hukumomin gwamnati.

Ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa kan kulawa na musamman da yake ba harkokin wasanni a jihar musamman ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United.

Haka kuma shugaban ƙungiyar ya yaba wa gwamna Raɗɗa da ya naɗa haziƙiin matashi Injiniya Surajo Yazid Abukur a matsayin kwamishinan harkokin wasanni a jihar da yace tuni harkokin wasanni suka fara ɗaukan sai ti.

Haka kuma ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa kan gyara filayen wasannin da gina wani a Charanci a inda yayi kira ga matasa su rinka ziyartan filayen wasannin damin motsa jikin su.

By ukarofi