Gwamnan Kano ya dakatar da buɗe makarantun jihar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da komawa makaranta ga daliban makarantun firamare da sekandire na zangon 2024/2025 bisa wasu dalilai da ba ta bayyana ba.

Daraktan wayar da kan al’umma na ma’aikatar Ilimi ta jihar, Balarabe Ƙiru ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Ya ce, Kwamishinan Ma’aikatar, Umar Doguwa ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan matsaloli ne da ake ƙoƙarin warware su da za su taimaka wajen inganta harkar ilimi a jihar.

A ranakun 8 da 9 ga watan Satumba ne aka shirya komawa makarantu don cigaba da karatu wanda a sakamakon ɗage lokacin ne, Ƙiru ya ce za a sanar da wani lokaci na komawa nan ba da jimawa ba.

Ya kuma yi kira ga ɗalibai da iyaye su kasance masu haƙuri da fahimtar su yayin da Ma’aikatar ke ƙoƙarin warware matsalolin da ke akwai a ɓangaren.

By Babaji