SERAP ta bai wa Shugaba Tinubu kwana biyu ya sauya tashin farashin fetur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ofishin tabbatar da ƴanci da adalci, SERAP ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya tsoma baki kan ƙara kuɗin man fetur da kamfanin man fetur na Ƙasa (NNPCL) ya yi, ya na mai nuna haramcin yin hakan da kuma bayyana shi a matsayin abu da aka yi ba bisa doka ba.

Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ya fitar a ranar Asabar, SERAP ya nemi shugaban ƙasa ya umarci NNPCL ya gaggauta cire ƙarin da ya yi akan farashin da ya ke a baya, kuma ya ɗauki matakin binciken rashawa a kamfanin.

SERAP ya nemi Antoni Janar na ƙasa, Mista Lateef Fagbemi da hukumomin kula da lamuran rashawa su gudanar da bincike akan zargin almundahana a NNPC.

Sannan, cikin abin da ya damuwa akan su, akwai batun Dala miliyan 300 da gwamnatin tarayya ta bai wa kamfanin a watan Agustan da ya gabata da Dala biliyan 6 na bashi da masu raba mai ke binsa da kuma batun rashin biyan harajin mai ga asusun ƙasa waɗanda ya kamata a yi bincike game da su.

SERAP ya ƙara da cewa, ƙarin farashin man fetur ɗin an yi shi ne ba bisa doka ba kuma hakan tauye haƙƙin Ɗan-adam ne.

Kazalika, ƙarin ya yi tasiri ga talakawa da waɗanda aka mayar da su saniyar ware a harkar gudanarwar ƙasar da kuma sanya talauci da rashin daidaito su ƙara faɗaɗa a Nijeriya.

By Babaji