
Daga BELLO A. BABAJI
Kwamitin ladabdtarwa na Jam’iyyar PDP ya karɓi rahoton kwamitin aikace-aikace na ƙasa (NWC) game da zargin ayyukan zagon-ƙasa na Ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu ƴan jam’iyyar.
Kwamitin, wanda tsohon Ministan Ma’aikatar harkokin wajen, Tom Ikimi ke jagoranta, ya gayyaci Wike da wasu jiga-jigan jam’iyyar ne zuwa gaban jagororinsa kan zarginsu da yi wa PDP zagon-ƙasa a lokacin zaɓen 2023.
Zargin ya mayar da hankali ne kan wasu gwamnonin PDP guda biyar waɗanda ake tuhumar su da yin zagon-ƙasa ga ɗan ƙarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar a jam’iyyar.
Gwamnonin na wancan lokacin sune; Wike – Ribas, Seyi Makinde – Oyo, Ifeanyi Ugwuanyi – Enugu, Samuel Ortom – Benue da kuma Okezie Ikpeazu na jihar Abia.
Mataimakin Sakataren hulɗa da jama’a na PDP, Ibrahim Abdullahi ya tabbatar da cewa mutane biyar ɗin tare da wasu, ana gayyatar su ne don fuskantar kwamitin ladabdtarwa da aka shirya musamman kan lamuran da suka shafi mambobin jam’iyyar.
Ya ƙara da cewa, kasancewar akwai ƙorafi kan cewa jam’iyyar ta daina aiki, ya sanya suka shirya kwamitoci biyu – ɗaya na sulhu, ɗaya kuma na ladabdtarwa, don haka suka buƙaci a yi hukunci game da batun.
