
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Litinin ne Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, lamarin da ke ƙara ƙarfafa jita-jitar sauya sheƙar gwamnan daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa APC mai mulki.
Rahotannin sun nuna cewa Abba ya isa ofishin shugaban ƙasar ne da misalin ƙarfe 4:13 na yamma.
Wannan ita ce ganawa ta musamman kuma ta farko da Shugaba Tinubu ya yi da wani tun bayan dawowarsa Nijeriya daga Abu Dhabi inda ya halarci taron harkokin ci-gaba na 2026.
Duk da cewa ba a bayyana abin da zaman nasu ya ƙunsa ba, ana ganin hakan a matsayin wani ci-gaba game da yiwuwar sauya sheƙar gwamnan zuwa APC.
Majiyoyi da ke kusa da tattaunawar sun shaida wa manema labarai cewa komawar Abba APC ta samu tsaiko ne bayan da jagorancin jam’iyyar ya ƙi amince wa buƙatar da gwamnan ya gabatar na neman tikitin tsayawa takarar gwamna kai-tsaye a zaɓen 2027.
Haka kuma, Gwamna Abba ya nemi jagorancim da ya bada sunan minista da zai wakilci jihar Kano a Majalisar Zartarwa ta Tarayya da kuma maye gurbin jami’an tarayya ‘yan Kano da masu masa biyayya.
Buƙatun, a cewar makusantan jam’iyyar, na neman kawo cikas ga shigar Abba APC musamman duba da cewa shi ma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin yana fakon tsayawa takarar gwamna a 2027.
Haka ma mai gidnasa na siyasa kuma jagoran Kwankwasiyya, wato Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya fito fili ya yi tir da shirin sauya sheƙar tare da gargaɗinsa da cewa akwai yiwuwar ya fuskanci ƙalubalen siyasa matuƙar ya fice daga NNPP.

