Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Yaran da suka kammala samun horan a cibiyoyin koyon sana’o’i guda tara sun fito daga sassa daban daban na jihar.
Yan matan sun koyi sana’ar ɗinki, ,saƙa,yin takalma, gyaran kai da sana’ar noma da sauran su.
Bikin bada tallafin ya gudana a Centre kuma sashin kula da ilimin ya’ya mata watau Department of Girl Child Education ƙarƙashin jagorancin babban daraktan Jamila Abdu Mani ta shirya.
A jawabinsa bayan da ya ƙaddamar da bada tallafin, gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana wannan shiri a matsayin ƙudirin gwamnatin sa ƙarfafa wa sana’o’i da kuma bunƙasa kasuwancan da tattalin arzikin jihar.
Ya bayyana cewa ka ba ya’ya mata ilimi ka kuma tallafa masu tamkar ka taimaka wajen cigaban al’umma,gwamnan ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tabbatar da cewa kowace ɗiya mace Ilimi ta kuma yi amfani da shi wajen cigaban al’umma.
Gwamnan ya sanar da cewa gwamnati na shirin tallafa wa wasu ya’ya 14000 a faɗin jihar nan bada jimawa ba.
Yayi kira ga waɗanda suka amfana da tallafi da suyi amfani da shi yadda ya dace,ya bayyana cewa gwamnati za ta cigaba da ba mata horo da tallafin kuɗi da kuma kayan aiki don bunƙasa kasuwancin da tattalin arzikin jihar.
A nata jawabin babban daraktan sashin ilimin ya’ya mata Hajiya Jamila Abdu Mani ta gargaɗi waɗanda suka amfana da tallafin da su guji karkatar ko sai da kayayyakin wanda hakan a cewar ta kaman cin amana ne.
