Gwamnan Kogi ya kaɗa ƙuri’arsa a Okene

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello tare da mai ɗakinsa, sun bi sahun sauran ‘yan Nijeriya wajen kaɗa ƙuri’arsu a bababban zaɓen da ke gudana a faɗin Nijeriya a wannan Asabar.

Bello ya kaɗa ƙuri’ar tasa ne a rumfar zaɓe ta 11 da ke Agasa Uvete, Okeneba, Okene.

Bayanai sun tabbatar Gwamnan ya isa rumfar zaɓen ne da misalin ƙarfe 9.40 na safe inda shi ma ha shiga layi ya tsaya a bayan waɗanda suka riga shi zuwa.

Bayan tantance shi da na’urar BVAS, Bello ya kaɗa ƙuri’arsa da misalin ƙarfe 10.

Jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri’ar tasa, Bello ya nuna ƙwarin gwiwarsa dangane da zaɓen inda ya ce yana da yaƙinin komai zai gudana cikin nasara a faɗin jihar.

Kodayake ya ce an samu rahoto kan cewa na’urar BVAS ta ƙi aiki yadda ya kamata a wasu wuraren, amma cewa an ɗauki matakin magance matsalar kuma komai na ci gaba da gudana.