Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rushe kasuwar Crystal Place da ke Ilorin mallakin tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Moshood Mustapha ya tayar da ƙura a Jihar Kwara.
Wannan lamarin ya ƙara dagula rashin jituwa tsakanin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaƙ da Mustapha waɗanda duk ’yan jam’iyya ɗaya ne.
An yi zargin an ruguza kadarorin ne a daren Lahadi inda ’yan sanda suka ba da tsaro. Mazauna rukunin sun yi ikirarin cewa Hukumar Kula da Tsarin ƙasa ta Jihar Kwara (KW-GIS) ta ba su sanarwar sa’o’i 3 a ranar Juma’a, bisa marya ƙa’ida. Sai dai shugaban KW-GIS, Suleiman Abdulkareem, ya bayyana cewa tun farko an bai wa Mustapha filin ne domin yin wurin ajiye motoci na kasuwanci.
“Amma ya ci gaba da kafa cibiyar kasuwanci kuma sabon binciken ya nuna cewa tsarin ya saɓa wa dokar da gwamnati ta ba mai shi a ranar 22 ga Maris, 2013.
“Gini ba bisa ƙa’ida ba yana haifar da cikas ga tsara birane, faɗaɗa hanyoyi da kuma kare muhalli waɗanda su ne muhimman abubuwan shirin sabunta birane na gwamnati,” inji shi.
Ya ƙara da cewa tun farko an tsara filin ne a matsayin koren wuri inda ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho da sauran jama’a suka sassauta a sabuwar sakatariyar jihar.
Hukumar ta ce an buƙaci masu haya da ke zama a shagunan da su kwashe kayansu, ta ƙara da cewa shirin sabunta biranen da ake ci gaba da yi yana da amfani ga jama’a.
Sai dai Mustapha a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Dokta Opeyemi Aregbesola ya fitar, ya yi watsi da ikirarin cewa tsarin ya saɓa wa amincewar farko.
Ya ce, amincewar da aka samu daga ofishin kula da filaye na jihar a shekarar 2013 na kasuwanci ne.
“An gina wurin Crystal Place da aka ruguje bisa tsarin ginin da aka amince da shi kuma ba a taɓa karya wata ƙa’idar gwamnati ba.”
