
Daga BELLO A. BABAJI
Kotun Ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin wata ƙaramar kotu da ta yi na haramta miƙa kasafin kuɗin Jihar Ribas na 2024 da ƴan Majalisar Dokoki huɗu suka yi.
Cikin hukuncinsa, Mai Shari’a Joseph Oyewole ya ce ɗaukaka ƙarar da Gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya yi da ke neman a soke hukuncin ranar 22 ga watan Janairu, ba shi da inganci.
Alƙalin, a lokacin da ya ke bayyana rashin halaccin kasafin Naira biliyan 800 da ƴan majalisa huɗun suka yi, ya ce tunda Fubara ya janye duka takardun da ya shigar game da ƙarar a karon farko na shari’ar, a yanzu ba shi da neman ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Da farko dai, Mai Shari’a Omotoso ya umarci Fubara ya sake baki ɗaya kuɗaɗen da ke mallaki ne na Majalisar Dokokin jihar tare da haramta masa shiga harkokinta.
Haka nan kotun ta umarci Sufeton ƴan sanda da rundunar baki ɗaya su cigaba da samar da tsaro ga ƴan Ribas wanda aciki har da ƴan Majalisar Dokokin jihar.
Kotun ta kuma yi umarni da a dakatar da rushe zauren Majalisar jihar da cewa za a gina sabo.
Har’ilayau, kotun ta haramta wa Majalisar ƙasa yin magana akan majalisar dokokin jihar da sauraron wata buƙata daga gwamnan jihar.
