Gwamnan Nasarawa ya sallami sakataren gwamnati da kwamishinoninsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya rushe Majalisar Zartarwar Gwamnatinsa inda ya tsige sakataren gwamnati da ilahirin tawagar kwamishinoninsa.

A ranar Juma’a, 3 ga watan Junairu ne gwamnan ya gabatar da hukuncin a yayin zaman Majalisar Zartarwa inda ya yi godiya gare su bisa ayyukan da suka yi wa gwamnati da mutanen jihar tare da musu fatan alheri.

An umarci tsigaggun kwamishinonin da su miƙa harkokin ma’aikatun da suka yi wa aiki da kayan gwamnati ga manyan sakatarorin ma’aikatun.

Haka nan shi ma sakataren gwamnati mai barin gado, ya miƙa ragamar aiki ga babban sakataren gudanar da harkokin muƙarraban gwamnati da ayyuka na musamman.

Wani babban jami’in gwamnati da ya buƙaci a sakaye sunansa, ya ce duk da cewa ba a bayyana dalilan da suka sa gwamnan ya ɗaukin matakin ba, amma sanannen abu ne cewa Gwamna A.A. Sule ya saba yin garambawul wa ma’aikatansa.

A shekarar 2021 ne Gwamna Sule ya rushe tawagar ma’aikatan gwamnatinsa don inganta harkokin gwamnati a jihar.

By Babaji