Gwamna Ƙaura ya shiga tsaka mai wuya bayan kasafin biliyan N3.4 ga fetur da tafiye-tafiye

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’iyyar PRP reshen Bauchi ta yi tir da shirin Gwamnatin jihar da Majalisar Dokoki na kashe sama da Naira biliyan 3.4 ga sanya fetur a ababen hawa, janaretoci da tafiye-tafiye a shekarar 2025 a matsayin abin kunya da rashin iya sarrafa dukiyar al’umma.

A cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Sakatarenta, Hon. Wada Abdullahi, jami’yyar ta ce lokaci ya yi da za a riƙa bibiyar masu riƙe da muƙaman gwamnati don tabbatar da cewa sun yi adalci a kowane mataki musamman ganin yadda al’umma suke fuskantar matsin tattali a jihar.

Ta ce yayin da iyalai suke gwagwarmayar ɗaukar nauyin gidajensu, gwamnatin ta mayar da hankali wajen almubazzaranci akan fifita buƙatar al’umma.

Baya ga Naira biliyan 1 da aka ware wa fetur na ababen hawa da janaretan gidan gwamnati, majalisa ta kuma buƙaci a ware biliyan 1.4 ga tafiye-tafiye.

PRP ta ce a madadin haka, za a iya gina asibitoci da makarantu da dama da waɗannan kuɗaɗen a matsayinsu na abin da suke buƙata ruwa a jallo.

Saboda haka ne jami’yyar da al’ummar jihar suke sanarwa da kuma kira ga Gwamna Bala Mohammed da mambobin Majalisar Dokokin jihar cewa ba su amince ba, don haka su ƙaurace wa sauya akalar dukiyar al’umma.

By Babaji