Gwamnan Zamfara ya jajenta wa waɗanda ambaliya ta rutsa da su a Gummi

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jajenta wa mutanen da haɗarin ambaliyar ruwan sama ya rutsa da su a ƙaramar hukumar Gummi da ke jihar.

A ranar Juma’a ne wani mamakon ruwan sama da aka yi a wasu yankunan ƙaramar hukumar ya ɓarnata gidaje da dama.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce gwamnan ya nuna damuwar matuƙa tare da tausayawa waɗanda al’amarin ya shafa inda ya ce ya na tattaunawa da masu-ruwa-da-tsaki tun bayan aukuwar lamarin da suka haɗa da; hukumomi, shugabannin da masu faɗa a ji a ƙaramar hukumar.

Ya ce, “Nan take na aika da tawaga daga gwamnatin jihar Zamfara zuwa ƙaramar hukumar domin duba halin da ake ciki tare da bayar da taimako na gaggawa ga waɗanda lamarin ya shafa.”

Ya kara da cewa, gwamnatinsa ta shirya tsaf wajen ganin an ɗauki duk wani mataki da ya dace wajen ganin irin haka bai faru ba a nan gaba tare da tabbatar da baki ɗaya mutanen da abin ya afka wa, sun samu taimakon da su ke buƙata.

By Babaji