Gwamnan Zamfara ya tabbatar da dokar hana zirga-zirgar babura a jihar

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar da wata babbar dokar taƙaita zirga-zirgar babura a jihar.

A ranar Alhamis ne gwamnan ya sanya hannu kan dokar a Fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.

Wata takarda da ta fito daga ofishin mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ta bayyana cewa jami’an tsaro sun yanke shawarar taƙaita zirga-zirgar babura a jihar ne yayin wani zama na gaggawa da su ka gudanar a ranar Laraba.

Sulaiman ya ce, domin tabbatar da halascin taƙaice zirga-zirgar, Antoni Janar na jihar, Abdul’aziz Sani (SAN) ya gabatar da dokar mai lamba ta 07, 2024 ga gwamnan wanda nan da nan ya ƙaddamar da ita.

Lokacin taƙaita zirga-zirgar shi ne daga ƙarfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe a faɗi jihar inda ta haramta hakan a kowace hanya, sannan wanda duk ya karya dokar, to zai haɗu da fushin hukuma.

Ya ƙara da cewa, wannan ƙoƙarin gwamnatin ne wajen bada kariya ga dukiya da rayukan al’umma gami da fuskantar ƙalubalen lamuran tsaro da kuma faɗaɗa hanyoyin magance matsalolin garkuwa da mutane da sauran su.

Kazalika, Antoni Janar ɗin na da ikon binciken duk wanda ya saɓa ma dokar.

By Babaji